A Rana Mai Kamar Ta Yau 4 Ga Watan Yuni 1996 Wasu ‘yan bindiga 6 su ka harbe Uwargidan Abiola, Kudirat Abiola, a kusa da gidanta a Legas.
A watan Mayun 1996, wata guda kafin a kashe Kudirat Abiola ba tare da Tausayi ba, an tsare ta na ƴan sa'o'i kaɗan bisa zargin mallakar wasu wallafe-wallafen sukar gwamnatin mulkin sojan Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Janar Sani Abacha. Duk da cewa mijin ta kuma hamshakin attajirin dan kasuwa, marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola, an daure shi a gidan yari bisa zarginsa da cin amanar kasa, Kudirat ta zama mai fafutukar neman Sa ma Masa ‘yancinsa. Kyakkyawar mace ce, da ta zama ɗaya daga cikin fitattun maƙiyan Gwamnatin Abacha.
A ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 1996, da misalin karfe 3:05 na rana a 7-Up Depot/Bus Stop a Ikeja, Marigayiya Kudirat Abiola tare da direbanta, wasu ‘yan bindiga shida sun Kai musu Farmaki. Raunin Bindiga Ya same ta da yawa, nan Take aka garzaya da ita Asibitin Eko domin neman agajin gaggawa. Duk kokarin da likitoci sukayi na ceto rayuwarta Abin ya ci tura. Kudirat Abiola ta rasu tana da shekaru 44 a duniya, bayan da wani harsashi ya samu goshinta. Shi ma direbanta bai tsira ba daga harin.
