Al'ummar Badawa, wani ƙauye da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Boɗinga ta jihar Sokoto na cikin wani yanayin da ya tilasta su yin kira ga hukumominsu da su kai musu dauki ta hanyar gyara musu asibitinsu wanda ya kwashe shekaru cikin mummunan hali.
Mazauna garin dai sun ce asibitin ya lalace ce bayan wata guguwa da ta yi awon gaba da wani ɓangare na asibitin shekaru 10 da suka gabata.Kuma tun wannan lokacin ne al'ummar garin suka ce aka yi banza da asibitin ba tare da samun gyara ba duk kuwa da ƙorafi da suka yi wa hukumomin lafiya.
Wani mazaunin garin na Badawa ya shaida wa BBC cewa " da dama da cikin ɗakunan ba su da rufi, katangun sun tsage sannan wasu sassan asibitin ne kawai ake amfani da su wajen kula da marasa lafiya."
Ya kuma ƙara da cewa hakan ya sa samun kulawar lafiya ya zama abu mai matuƙar wahala ga al'ummar yankin musamman marasa lafiya.
Mazauna garin sun ce dubban marasa lafiya na ziyartar asibitin a kowane wata.