An Kaddamar Da Cibiyar Sarrafa Gari Da Rogo A Batsari Ta Katsina

 Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Malam Dikko Umaru Radda Ph,D, ya ƙaddamar da Cibiyar Sarrafa Gari da Rogl a Ƙaramar Hukumar Batsari, inda ya raɗa ma cibiyar suna da "Dr. Abba Sayyadi Ruma Cassava Processing Center." An ƙaddamar da Cibiyar ne tare da sanya mata wannan suna ne domin girmama marigayi tsohon Ministan Noma da Albarkatun Ruwa. Gwamnan ya bayyana cewa aikin ƙaddamarwar yana daga cikin manufofin gwamnatinsa na bunƙasa noma, samar da ayyukan yi da rage talauci a ƙarƙashin shirin Building Your Future Agenda.

Gwamna Malam Dikko Radda ya ce noma shi ne ginshiƙin tattalin arziƙin Jihar Katsina, ya ƙara jaddada cewa ƙara ɗaga darajar amfanin gona ta hanyar sarrafawa, adanawa da bunƙasa masana’antun noma na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa. Ya ce cibiyar za ta rage asarar amfanin gona bayan girbi, ta ƙara kuɗin shiga ga manoma tare da samar da guraben ayyukan yi musamman ga mata da matasa.

Gwamnan ya buƙaci manoma, da  ƙungiyoyin mata da matasa su kula da cibiyar tare da amfani da ita yadda ya kamata domin al’umma su ci gajiyarta. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin noma ta hanyar samar da ingantattun iri da kayan aikin noma na zamani, ban ruwa da sauran muhimman abubuwan more rayuwa a yankunan karkara.

Da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Harkokin Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA), Dakta Babangida Kabir Ruma, ya ce: "Cibiyar za ta ƙarfafa fito da darajar rogo sosai, tare da samar da ayyukan yi, za kuma ta rage asarar amfanin gona bayan girbi tare da bunƙasa sana’o’in da suka shafi sarrafa rogo a faɗin jihar. Ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa tattalin arzikin manoma da 'yan kasuwa.

A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Joɓe, da Shugaban Ƙaramar Hukumar Batsari, Hon. Mannir Mu’azu, sun yaba da aiki da kuma ƙaddamar da cibiyar da aka yi, suna mai cewa za ta inganta tattalin arziƙin yankin da rayuwar al’umma. Bikin ƙaddamarwar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, abokan hulɗar ci gaba, shugabannin al’umma, manoma, ƙungiyoyin mata da wakilan matasa, da sauran jama'a.


Post a Comment

Previous Post Next Post