An Ƙaddamar Da Horas Da Masu Kanana Da Matsakaitan Sana'o'i Guda 300 A Batsari

Bayan kammala buɗe masana'antar sarrafa Rogo da Gari a ƙaramar Batsari. Hukumar Bunƙasa Kasuwanci ta Jihar Katsina, KASEDA, tare da haɗin gwiwar Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNDP, sun fara horas da sama da masu ƙanana da matsakaitan sana'o'i har 300 dangane da dabarun gudanar da kasuwanci da kuma inganta kuɗaɗen shiga.

An ƙaddamar da shirin ne a Ƙaramar Hukumar Batsari, sai dai mahalarta taron sun fito ne daga ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Batsari, Charanchi, Malumfashi, Matazu da kuma Faskari.

Babban Daraktan KASEDA, Dakta Babangida Kabir Ruma, ya ce horaswar ta yini biyu ce, kuma tana gudana ne a ƙarƙashin shirin bunƙasa yankin Arewa maso Yamma da haɗin gwiwar UNDP da Gwamnatin Jihar Katsina. Ya ƙara da cewa shirin na bana ya biyo bayan nasarorin da aka samu a shekarar 2024, wanda ya sa UNDP ta amince da faɗaɗa shi domin ƙarin al'ummomi su amfana.

Dakta Babangida Kabir Ruma ya ƙara da cewa bayan kammala horaswar, waɗanda suka cika sharuɗɗan shirin za su samu tallafin jari, inda wasu za su karɓi naira dubu 320 tare da yi musu rajistar Hukumar CAC kyauta, yayin da wasu kuma za su samu tallafin naira dubu 150 ƙarƙashin haɗin gwiwar KASEDA da UNDP, domin gina kawunansu.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa al'ummomin yankunan da matsalar tsaro ta shafa ta hanyar samar da shirye-shiryen da za su bunƙasa tattalin arzikinsu.

Ya kuma buƙaci mahalarta su yi amfani da ilimin da za su samu domin faɗaɗa kasuwancinsu, domin a ƙara samun kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwarsu.

Masana da suka gabatar da darussan sun bayyana cewa kyakkyawan tsarin gudanar da kasuwanci na taimakawa wajen bunƙasa sana'o'i, ƙara yawan ciniki da tabbatar da samun riba mai ɗorewa, tare da koya wa mahalarta dabarun gudanarwa da ingantattun hanyoyin tallata hajojinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post