Za A Dauki Sabbin Ma'aikata Sojojin Kasa Har Dubu 28,000



FADAR SHUGABAN ƘASA ƘARƘASHIN JAGORANCIN SHUGABA BOLA AHMAD TINUBU YA AMINCE DA FAƊAƊA TSARIN SOJIN NIJERIYA ZUWA RABO 12, TARE ƊAUKAR SABBIN SOJOJI 28,000 DOMIN ƘARFAFA TSARON ƘASA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Tarayyar Najeriya, ya amince da faɗaɗa tsarin Sojin Najeriya daga rabo 8 zuwa 12 wani mataki na tarihi domin inganta tsarin tsaron ƙasa da haɓaka ƙarfin aiki na Sojin Nijeriya.

Wannan amincewa na nuna ƙudurin Shugaban ƙasa na tabbatar da bai wa rundunar sojoji kayan aiki don fuskantar sabbin ƙalubalen tsaro da ke tasowa a Nijeriya yadda ya kamata, da kuma ƙara ƙarfin kare ƙasa.

Faɗaɗar ta biyo bayan ci gaba da zuba jari da wannan gwamnati ke yi a fannin sojoji, ciki har da amincewa da ɗaukar sabbin sojoji guda dubu 28,000, tare da siyan kayan yaƙi masu mahimmanci, inganta jin daɗin sojoji, da kuma ci gaba da tallafawa shirye-shiryen aiki da zamani na rundunar.

A ƙarƙashin sabon tsarin, Sojin Najeriya za su kasance da rabo 12 da aka shimfiɗa a faɗin ƙasar kamar haka:

1.  HedikwatarTsaro na 1 Kaduna (Jihohin Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa)
2.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 2 Ibadan (Jihohin Oyo, Osun, Ekiti da Ondo)
3.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 3 Jos (Jihohin Filato, Bauchi da Gombe)
4.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 5 Makurdi (Jihohin Benue, Nasarawa da Kogi)
5.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 6 Port Harcourt (Jihohin Rivers, Akwa Ibom da Cross River)
6.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 7 Maiduguri (Jihohin Borno da Yobe)
7.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 8 Sokoto (Jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara)
8.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 9 Ilorin (Jihohin Kwara da Neja)
9.  Hedikwatar Tsaro Rabo na 10 Jalingo (Jihohin Taraba da Adamawa)
10. Hedikwatar Tsaro Rabo na 81 Legas (Jihohin Legas da Ogun)
11. Hedikwatar Tsaro Rabo na 82 Enugu (Jihohin Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi da Imo)
12. Hedikwatar Tsaro Rabo na 83 Benin City (Jihohin Edo, Delta da Bayelsa)

Kafa sabbin rabe-raben a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City zai inganta umarni da iko, ta hanyar raba ikon yanke shawara na aiki, tare da ƙarfafa tsaron iyakoki, da kuma inganta kare muhimman ababen more rayuwa na ƙasa, ya inganta yaƙi da ta’addanci da tsaron cikin gida, sannan ya tabbatar da saurin amsa kiran sojoji ga barazanar da ta taso a faɗin ƙasa.

Aiwatar da sabon tsarin zai kasu kashi biyu.  
Kashi na ɗaya, wanda ya haɗa da kafa Rabo na 5, 9, da 10 da kuma sake tsara rundunonin da ake da su, wanda za a kammala shi nan da watan Satumba 2026.  

Kashi na biyu, wanda ya haɗa da kafa Rabo na 83 da ƙarin sake tsarawa, ana sa ran za a kammala shi nan da watan Disamba na shekarar 2026.

Shugaba Tinubu ya yaba wa Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da dukkan jami’ai da sojojin Nijeriya bisa sadaukarwa, ƙwarewa, da jajircewarsu wajen kare iyakokin mallakar Nijeriya da cikinta.

Shugaban ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da zuba jari a Rundunar Sojoji, domin tabbatar da cewa suna da isasshen kayan aiki, suna da ƙwazo, kuma suna da cikakkiyar ƙarfin kare ƙasa da tabbatar da tsaron kowa da kowa a Najeriya.

Bayo Onanuga 
Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman  
(Harshen Gida & Dabarun Sadarwa)  
23 ga Yuli, 2026

Post a Comment

Previous Post Next Post