Mata Dubu 57, Sun Tara Zunzurutun Kudi Kimanin Miliyan 349 Daga Cikin Kudaden Da Suke Ajiyewa Duk Sati Karkashin Tsarin NFWP-SU

Ƙara Faɗaɗa Aikin "Nigeria for Women Project" a Jihar Katsina

Mai girma Gwamnan jihar Katsina Malam Umaru Dikko Radda ya ƙarfafi gwiwar mata dangane da shirin Nigeria for Women Project inda ya ce: 
"Ƙarfafa mata ɗaya ne daga cikin mafi kyawun jarin da kowace al'umma za ta iya yi. Idan mata suka sami dama a fannin tattalin arziƙi, iyalai za su samu kwanciyar hankali, yara za su samu kulawa da ilimi mafi kyau, kuma al'ummomi za su samu ci gaba mai ɗorewa.

Jiya a Daura, na sami damar yin mu'amala ta kai tsaye da masu cin gajiyar shirin Nigeria for Women Program Scale-Up (NFWP-SU) kuma na gani da idona tasirin da wannan shiri ke yi a rayuwar dubban mata a faɗin Jihar Katsina.

Abin da na gani ya burge ni. A faɗin ƙananan Hukumomin Katsina, Daura da Funtua, mata sama da 57,000 sun haɗu a cikin ƙungiyoyin haɗin gwiwa, sun rungumi al'adar ajiya, sun ƙarfafa kasuwancinsu kuma bakiɗaya sun tara sama da Naira Miliyan 349 ta hanyar gudunmawar da suke bayarwa kowane mako.

A Daura kaɗai, kusan mata 19,000 suna shiga cikin ƙungiyoyi 765 na haɗin gwiwa. Ƙudurinsu, horo da jajircewarsu sun nuna cewa idan aka ba su goyon baya da ya dace, matanmu za su iya cim ma abubuwa masu ban mamaki kuma su ba da gudummawa mai girma wajen bunƙasa tattalin arzikin jiharmu."

Ya ci gaba da cewa:

"Wannan nasara ta ƙarfafa imaninmu cewa ƙarfafa mata ba wai alhakin zamantakewa ba ne kawai ba, har ma jari ne na dabaru domin makomar Jihar Katsina. Saboda haka ne gwamnatinmu ta bayar da Naira Biliyan 4 a matsayin tallafin gwamnati na shirin kuma ta himmatu wajen ganin an aiwatar da shi cikin nasara."

Mai girma Gwamnan ya bankaɗo irin nasarorin da aka samu a shirin, inda ya ce:
"Dangane da nasarorin da aka samu zuwa yanzu, mun ƙuduri aniyar faɗaɗa shirin daga Kananan Hukumomi 3 na gwaji zuwa dukkan ƙananan Hukumomi 34 na jihar, domin tabbatar da cewa ƙarin mata sun sami damar da tallafin da suke buƙata domin bunƙasa. Nasarar da wannan shiri ya samu ta sanya muka fara nazarin tsarin da zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arziƙin maza, domin tare za mu iya gina iyalai masu ƙarfi, al'ummomi masu juriya da Jihar Katsina mai wadata."

Gwamnan Katsina ya ƙara da cewa: "Ina yabawa mata masu cin gajiyar shirin bisa jajircewa da juriyarsu, kuma ina godiya ga abokan aikinmu, masu gudanarwa da dukkan masu ruwa da tsaki da ƙoƙarinsu ke ci gaba da sa wannan shiri ya yi nasara."

Post a Comment

Previous Post Next Post