Arewa Ta Rasa Tsoffin Kimominta, Shi Ya Haddasa Talauci Da Rashin Tsaro – Ango Abdullahi, Bugaje


Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Arewa (Northern Elders Forum), kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ango Abdullahi, tare da masanin tattalin arziki da siyasa, Dakta Usman Bugaje, sun bayyana cewa Arewa ta yi nesa da kyawawan ɗabi'u da salon shugabanci da suka gina martabarta a baya. 

Sun ce taɓarɓarewar tsaro, ƙaruwar talauci da koma bayan ci gaba a yankin sun samo asali ne daga barin kyawawan ƙa'idoji da manufofin shugabannin farko na Arewa.

Sun yi wannan jawabi ne a taron tunawa karo na uku da marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna, mai taken: "Daga Sadaukarwa Zuwa Tsari: Farfaɗo da Manufofin Janar Hassan Usman Katsina Domin Samun Arewa Mai Wadata."

A nasa jawabin, Farfesa Ango Abdullahi ya ce Arewa, wadda a da ta yi fice wajen gaskiya, biyayya, ladabi da kishin ci gaba, ta rasa waɗannan kyawawan ɗabi'u.

Ya ce, "Arewa ta rasa ƙimominta. Ko da ba ku son jin haka, wannan ita ce gaskiyar lamarin. Da ba mu rasa kyawawan ɗabi'un da muka gada daga iyayenmu da shugabanninmu na farko ba, da Arewa ba ta kai wannan matsayi ba."

Ya bayyana cewa duk da yadda biranen Arewa suka bunƙasa ta fuskar gine-gine, halaye irin su gaskiya, sadaukarwa, kishin ƙasa da shugabanci na gaskiya sun ragu matuƙa.

"Arewa tana cikin wani mawuyacin hali. A ganina wannan ne babban dalilin da ya sa yankin ya tsaya cak wajen ci gaba. Ba gine-ginen da ake gani ne matsala ba, babban abin da ya jefa Arewa cikin wannan hali shi ne rasa kyawawan ɗabi'unmu," in ji shi.

Ya buƙaci al'ummar Arewa su yi koyi da rayuwar marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wanda ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka kasance abin koyi wajen riƙon amana, gaskiya da sadaukar da kai wajen hidimar jama'a.

Ya ƙara da cewa idan aka koma ga waɗannan ƙimomi, babu shakka Arewa za ta kasance cikin wani yanayi mafi alheri fiye da yadda take a yau.

A nasa jawabin, Dakta Usman Bugaje ya ce Arewa ta shafe shekaru tana fama da durƙushewar tattalin arziki, rashin tsaro da lalacewar cibiyoyin gwamnati saboda ta kauce daga irin hangen nesa da shugabanci irin na Janar Hassan Usman Katsina da takwarorinsa.

Ya ce matsalolin Arewa sun haɗa da raguwar noma, tarwatsa dubban mutane daga gidajensu, durƙushewar tattalin arziki, ƙaruwar talauci, lalacewar ilimi da kiwon lafiya, tare da raguwar ingancin albarkatun ɗan Adam.

Bugaje ya ce rashin tsaro na ci gaba da kawo cikas ga noma, kasuwanci da hanyoyin samun abin dogaro da kai a faɗin yankin.

Ya tambaya, "Yanzu nawa ne ya rage daga cikin Arewa? Ko kuma nawa ne ya rage daga cikin hankalin shugabanninmu, musamman waɗanda ke gwamnati? Ina shugabannin irin Janar Hassan Katsina da za a kai ƙorafi gare su? Ina shugabanci? Ina alkibla?"

Ya kuma soki wasu daga cikin manyan Arewa da ke ta bayyana damuwa kan halin yankin ba tare da gabatar da mafita ta zahiri ba.

"A yau ya zama tamkar abin shaƙatawa ga wasu daga cikin manyan Arewa su zauna cikin jin daɗi suna cewa Arewa tana cikin matsala, wasu ma suna cewa Arewa ta lalace gaba ɗaya. Irin waɗannan kalamai na nuna sakaci ko ma hannu a cikin matsalolin da yankin ke fuskanta," in ji shi.

Bugaje ya kuma tuna wata ganawa da ya yi da marigayi Janar Hassan Katsina bayan tsohon jakadan Amurka ya kai ƙorafi kan wani maƙala da ya rubuta yana sukar mulkin mallaka na ƙasashen Yamma.

Ya ce maimakon Janar Hassan Katsina ya hana shi rubutu, sai ya ƙarfafa masa gwiwa ya ci gaba da rubuta irin waɗannan maƙalun.

"A lokacin da ya tabbatar abin da nake yi daidai ne, sai ya ce in ci gaba da rubutu. Wannan shi ne irin shugabancin da suka yi," in ji Bugaje.

Ya bayyana cewa ƙarni na Janar Hassan Katsina ya haɗa ilimin zamani da kyawawan al'adun Arewa kamar gamsuwa da abin da aka samu, ladabi, bin doka, adalci, tawali'u da sadaukarwa ga ci gaban al'umma.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga shugabannin siyasa na wannan zamani da su dawo ga waɗannan ƙimomi domin shawo kan matsalolin zamantakewa, tattalin arziki da rashin tsaro da suka addabi Arewa.

An shirya taron tunawar ne domin girmama gudummawar marigayi Janar Hassan Usman Katsina tare da ƙarfafa tattaunawa kan shugabanci, mulki nagari da makomar Arewa.

Post a Comment

Previous Post Next Post