Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ta zo ƙarshe, yana mai cewa ba ya son ci gaba da mu'amala ko tattaunawa da gwamnatin Iran.
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai tare da Babban Sakataren ƙungiyar tsaron NATO, Mark Rutte.
Ya ce a ra'ayinsa batun tsagaita wutar ya ƙare, tare da zargin shugabannin Iran da kasancewa masu tsattsauran ra'ayi da kuma cewa idan suka mallaki makamin nukiliya za su yi amfani da shi.
Har ila yau, Trump ya nuna shakku kan yiwuwar ci gaba da tattaunawar nukiliya da Iran, yana mai cewa zai tuntubi tawagarsa ta masu sasantawa, amma ya bayyana cewa ci gaba da tattaunawa da jami'an Iran bata da amfani saboda, a cewarsa, ba sa cika alkawari.
A cewar Trump, jami'an Iran kan amince da wasu sharuɗɗa a sirrance yayin tattaunawa, amma daga baya su fito su musanta hakan a bainar jama'a.
Duk da cewa ya ce ana iya ci gaba da tattaunawar a hukumance, Trump ya jaddada cewa a ganinsa batun ya ƙare.
Wannan na zuwa ne yayin da rikici tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari.
Rahotanni sun ce Amurka ta kai hare-hare kan wurare 80 a Iran, yayin da dakarun Islamic Revolutionary Guard Corps na Iran suka mayar da martani da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka guda 85 da ke ƙasashen Bahrain da Kuwait.
