Barayin Daji Sun Kashe Mai Unguwa A Yankin Kano

Kamar yadda ya sha alwashi, shugaban ɓarayin daji na yankin Musawa da Matazu Kachalla Muhammadu, wanda Manjo Janar Rabe Abubakar ya rasu a shingensa, jiya da yammacin Litinin ya kai sumame a yankunan Kano kamar yadda ya ɗauki alƙawari a wani faifan audio na waya da ya karaɗe soshal midiya, inda ya kashe Yusuf Adamu mai unguwar Taka Tsaba da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.

Kachalla Maha da yaransa sun saci shanu a ƙauyen 'Yan Kamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa, sai dai jami'an sojoji da haɗin gwiwar 'yan sa kai da na C-Watch sun yi galaba a kan ɓarayin a fafatawar da suka yi, inda aka tabbatar da an yi wa wasu daga cikin ɓarayin raunuka Sannan kuma an tabbatar da an ƙwace dukkan shanun da suka sata, kana aka rako su, suka ranci na kare.

Sai dai lokuta da yawa, ana bayar da rahoton fitowar ɓarayin daji a yankunan Funtua da Matazu da Malumfashi da Ƙanƙara da Musawa da Neja da Zamfara da kusan dukkan sassan da matsalar rashin tsaro ta fi ƙamari, amma da yawan mutane suna yin kunnen uwar shegu da batun, wanda hakan yake ƙara jefa rayukan mutane cikin haɗari, ya kamata ko ba komai idan aka ce a kula sun yi wajen ƙauyenku a ƙalla ko ba ka yi komai ba, ka ɗauki matakin kare kanka, idan ma so samu ne ka yi ƙoƙarin hana su wucewa ko da kuwa zai kai ku ga mayar da wuta ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post