Tarihi ya maimaita kansa, ga duk wanda ya kalli wasan da aka fafata a daren jiya tsakanin England da Argentina ya San lallai Argentina ba wasa suka fito ba, yaƙi suka fito kamar yadda suka sha alwashi, kuma kwalliya ya biya kuɗin sabulu.
Irin yadda Argentina ta warwasa a wasan tare da hana 'yan wasan England kataɓus shi ne ya ba su damar yin nasara a kansu, duk da cewa, England ce ta fara saka ƙwallo a ragar Argentina, amma hakan bai ƙaryar masu da gwiwa ba, maimakon haka na sai jagoran wasan Argentina Lionel Messi ya fito da sabon salo tare da barin tsakiya ya koma ɓangaren gaba na dama (7) ya ci gaba da aiko da muna nan saƙonnin da suka rikita Ingilawa, har dai suka samu suka dawo cikin wasan bayan da shi dai Messi ɗin ya taimaka wa Enzo Fernandez da ƙwallon da ya saka raga.
Bayan wasu mintinan kuma ba jimawa, Messi ya sake taimakawa Lautaro Martinez ya jefa tashi ƙwallon a cikin mintina 3 daga 7 da aka ƙara domin ƙarƙare wasan, wanda hakan ya ba su nasarar tsallakawa zuwa zagayen ƙarshe na gasar cin kofin duniya, inda za su kece raini da ƙasar Sifaniya.
Idan dai ba mu manta ba, muna sane da cewa, a yanzu haka ƙasar ta Argentina ita ce wadda take riƙe da kambun lashe gasar kofin duniyar da ta gabata wadda aka yi a Qatar a shekarar 2022, wanda suka fafata da ƙasar Faransa a lokacin.