A ranar Asabar mai zuwa ne za a sake fafatawa a filin Miami da ke jihar Florida ta ƙasar Amurika domin fitar da wanda zai lashe na 3 a gasar cin kofin duniya na 2026 tsakanin Ingila da Faransa.
Waɗannan ƙasashe ba ranar Asabar ne za su fara fafatawa ba, a'a akwai gwabzawa da gwajin ƙwanji da suka yi har sau 3 a wasannin cin kofin duniya mabambanta, ke nan wannan shi ne karo na 4 da za su sake karawa a Amaurika.
Duk da kusancin yanki da kuma tarihin hamayya na ƙarni da dama, ƙasashen biyu na fuskantar juna sau uku kacal a babban dandalin ƙwallon ƙafa na duniya. Idan ana batun hamayyar ƙwallon ƙafa a nahiyar Turai da ma duniya bakiɗaya, ba za a taɓa barin ƙasashen Faransa da Ingila a baya ba. Sai dai kuma, abin mamaki shi ne yadda waɗannan manyan ƙasashen biyu maƙwabta ba su cika samun damar gogayya da juna ba a gasar cin kofin duniya (FIFA World Cup).
A cikin sama da shekaru casa'in na tarihin wannan gasa, ƙasashen biyu sun fuskanci juna sau uku kacal. Kowace haɗuwa tana ɗauke da labari na musamman da kuma tarihin da masoya ƙwallon ƙafa kafa ba za su taɓa mantawa da shi ba.
1966: Mamayar Ingila A Gida
Haɗuwarsu ta farko ta faru ne a shekarar 1966, a lokacin da Ingila ta karɓi bakuncin gasar. Ƙasashen biyu sun fafata ne a rukunin farko a shahararren filin wasa na Wembley dake birnin Landan.
Ingila ta samu nasara mai sauƙi da ci 2-0, inda shahararren dan wasan gaba na lokacin, Roger Hunt, ya zura ƙwallaye biyun. Wannan nasara ta taimaka wa Ingila wajen samun gurbin zuwa zagaye na gaba, har ta kai ga lashe kofin duniya na farko kuma guda ɗaya tilo da take tinƙaho da shi zuwa yau.
1982: Robson Ya Girgiza Faransa
Bayan shekaru 16, ƙasashen biyu sun sake haɗuwa a ƙasar Sifaniya a zagayen farko na rukunoni. Wannan wasa ya kafa tarihi na musamman tun kafin a daɗe ana fafatawa.
Ɗan wasan tsakiya na Ingila, Bryan Robson, ya zura ƙwallon farko a ragar Faransa a cikin sakan 27 kacal da fara wasa wadda ta kasance ƙwallo mafi sauri a tarihin gasar a wancan lokacin. Robson ya sake zura ƙwallo ta biyu, sannan Paul Mariner ya cike ta uku, inda Ingila ta tashi da nasara da ci 3-1, duk da ƙwallo ɗaya tilo da Gerard Soler ya ci wa Faransa.
"Kwallon da Bryan Robson ya ci a cikin sakan 27 a shekarar 1982 ta kasance ɗaya daga cikin manyan al'ajabi na tarihin hamayyar ƙasashen biyu."
2022: Ɗaukar Fansar Faransa A Qatar
Sai a shekarar 2022 haɗuwarsu ta uku ta kasance, kuma ita ce mafi muhimmanci domin sun haɗu ne a matakin fitar da gwani (Quarter-finals) a ƙasar Qatar. Wannan shi ne karon farko da Faransa ta samu galaba a kan Ingila a gasar kofin duniya.
Aurélien Tchouaméni ya fara jefa ƙwallo mai ƙayatarwa daga nesa, kafin daga baya kaftin ɗin Ingila, Harry Kane, ya rama ta bugun fanareti. Sai dai kuma, ƙwararren ɗan wasan gaba na Faransa, Olivier Giroud, ya sake jefa ƙwallo ta biyu da kai. Ingila ta samu damar daidaita wasan a ƙarshe ta hanyar wani fanaretin, amma Harry Kane ya harba ƙwallon sama, wanda hakan ya kawo ƙarshen fatan Ingila a gasar, Faransa kuma ta tsallaka zuwa wasan karshe inda suka fafata da Argentina.