Pyelonephritis wata mummunar cutar kamuwa da ƙwayoyin cuta a koda ce. Yawanci tana farawa ne daga cutar mafitsara (UTI) wadda ba a kula da ita ba, sai ƙwayoyin cutar su haura su kai ga koda. Wannan cuta na buƙatar kulawa ta gaggawa, domin idan aka yi sakaci, tana iya jawo babbar illa ga lafiya.
Cuta ce da ke faruwa idan ƙwayoyin cuta (bacteria) suka shiga mafitsara, suka bi hanyar fitsari suka kai ga koda.
Ta fi yawan faruwa a:
~ Mata (saboda gajeriyar hanyar fitsari)
~ Masu juna biyu
~ Masu ciwon siga (diabetes)
~ Mutanen da ke da matsalar fitsari
Alamomin Pyelonephritis:
Alamomin na iya bayyana cikin gaggawa, kuma sun haɗa da:
~ Zazzabi mai tsanani
~ Rawar jiki da sanyi
~ Ciwon ƙugu ko bayan baya (ƙasan baya) ~ Ciwon ciki
~ Fitsari mai zafi ko radadi
~ Yawan fitsari
~ Fitsari mai wari ko gauraye da jini
~ Tashin zuciya da amai
~ Kasala da rashin ƙarfi
👉 Idan waɗannan alamomi sun bayyana, kar a jira su wuce da kansu, ayi sauri aje asibiti.
Me Ke Jawo Pyelonephritis?
Manyan dalilai sun haɗa da:
~ Rashin magance cutar fitsari (UTI) da wuri
~ Rike fitsari a mafitsara na dogon lokaci
~ Dutse a koda ko mafitsara
~ Amfani da catheter (bututun fitsari), ba tare tsafta mekyeu ba.
~ Ciki (juna biyu)
~ Raunin garkuwar jiki
Pyelonephritis a Lokacin Ciki:
Ga mace mai ciki, wannan cuta na da hatsari sosai, domin tana iya jawo:
~ Haihuwa kafin lokaci
~ Rage lafiyar jariri
~ Tsananin rashin lafiyar uwa
Saboda haka, duk wata mai ciki da ta ji:
~ zazzabi
~ ciwon baya
~ fitsari mai zafi
Ta gaggauta zuwa asibiti.
Yadda Ake Ganowa (Diagnosis)
Likita na iya:
~ Gwajin fitsari
~ Gwajin jini
~ Yin hoton koda (ultrasound ko CT scan)
~ Binciken ƙwayoyin cuta (culture)
Yadda Ake Magani;
Maganin Pyelonephritis yawanci ya haɗa da:
~ Shan maganin kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics wanda ya dace da jikin ka)
~ Shan ruwa da yawa akai akai
~ A wasu lokuta, kwanciya a asibiti
Kada a taɓa shan magani da kai ba tare da shawarar likita ba.
Yadda Za a Kare Kai
~ A rika shan ruwa sosai
~ Kada a riƙe fitsari na dogon lokaci
~ A rika tsaftar gaba
~ A nemi maganin UTI da wuri idan anji alamu
~ Mata su kula sosai a lokacin ciki
