Jihar ta ware zunzurutun kuɗi kimanin Naira Biliyan 100 ga aikin gona a kasafin kuɗin 2026, wanda hakan ya zarce ƙa'idar Malabo
Gwamnatin Jihar Kaduna ta gudanar da taron ƙaddamar da rabon taraktoci da kuma tirela 500 ta takin zamani da kuma kayan aikin gona na zamani ga manoma ƙanana, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɓaka abinci da yawan amfanin gona a jihar.
Mai girma Gwamna Sanata Uba Sani, CON, ne ya ƙaddamar da shirin a filin taro na Murtala Square dake Kaduna a ranar Asabar. Ya ce wannan tallafi na shirin Noman Rani na 2026 zai amfani manoma kimanin dubu ɗari da hamsin (150,000) kai tsaye a cikin ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar.
Yayin jawabi a wurin taron da ya samu halartar jama'a da yawa, Gwamna Sani ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar sauya aikin gona daga wani abu na lokaci-lokaci zuwa ginshiƙi na canza tattalin arziƙin jihar.
"A cikin kasafin kuɗin 2026, mun ɗaga kaso da ake bai wa aikin gona daga Naira Biliyan 1.48 a 2023 zuwa sama da Naira Biliyan 100. Wannan ya kai kusan kashi 11.65% na kasafin kuɗin jihar gabaɗaya, wanda hakan ya zarce ƙa'idar bayar da kaso ga aikin gona ta Malabo," in ji Gwamnan.
Ya bayyana cewa a cikin yanayin noma biyu da suka wuce, gwamnati ta raba taraktoci sama da 900 da taki. Ya ƙara da cewa manoma sama da 69,000 sun ci gajiyar shirin Tallafin Noma na (A Koma Gona), yayin da manoma sama da 100,000 kuma ke jin daɗin inshorar gonaki.
"Yayin da tsaro ke ci gaba da samun ingantawa, dubban manoma sun dawo filayensu da ƙarfin gwiwa," in ji Sani. "Wannan ya tabbatar mana cewa tsaro da wadataccen abinci abubuwa ne masu tallafawa juna wajen samun ci gaba mai ɗorewa."
Gwamnan ya kuma yi godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa goyon bayansa na dindin ga Jihar Kaduna.
Ya ce: "Burinmu na nan take shi ne gina tattalin arziƙin aikin gona na zamani, mai ƙarfi da zai iya fafatawa a duniya, wanda zai tabbatar da wadataccen abinci, samar da ayyukan yi, rage talauci da kawo wadata ga mutanen Jihar Kaduna."