Abuja – Ministan Ilimi na Tarayya, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da bincike a gidajen al'umma a faɗin Najeriya domin gano ainihin adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na 2026 na Ƙungiyar Wakilan Labaran Ilimi ta Najeriya (ECAN) da aka gudanar a Abuja, inda ya ce Ma'aikatar Ilimi ta haɗa kai da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) domin tattara sahihan bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofi da shirye-shiryen bunƙasa ilimi.
A cewarsa, binciken zai ba gwamnati damar fahimtar girman matsalar da kuma tsara hanyoyin magance ta yadda ya kamata. Ya ƙara da cewa duk da mayar da sama da yara miliyan ɗaya zuwa makaranta cikin shekaru biyu da suka gabata, har yanzu ana buƙatar ingantattun bayanai domin auna ci gaban da aka samu.
Ministan ya kuma buƙaci 'yan jarida su ƙara mayar da hankali kan aikin bincike, yana mai cewa sahihan bayanai za su ƙarfafa gaskiya da inganta harkar ilimi a Najeriya.