Shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta yi watsi da zargin da wasu jami'an Amurka suka yi cewa gwamnatinta na da alaƙa da manyan ƙungiyoyin dillalan miyagun ƙwayoyi (cartels), tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya, marar tushe kuma abin ƙi.
Da take magana a wani taron manema labarai, Sheinbaum ta ce gwamnatin Mexico ta himmatu wajen yaƙi da ayyukan ta'addanci da na ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi. Ta bayyana cewa gwamnatinta ta ƙara kaimi wajen gudanar da hare-hare da kama mambobin waɗannan ƙungiyoyi a sassa daban-daban na ƙasar.
Ta jaddada cewa ba za ta lamunci cin hanci ko haɗin kai tsakanin jami'an gwamnati da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ba.
Kalaman nata sun biyo bayan zargin da wasu jami'an Amurka suka yi cewa akwai wasu ɓangarori na gwamnatin Mexico da ke da alaƙa da ƙungiyoyin cartels, lamarin da ya ƙara tsananta rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu.
Sheinbaum ta ce irin waɗannan zarge-zarge na iya kawo cikas ga kyakkyawar haɗin gwiwar da ke tsakanin Mexico da Amurka wajen yaƙi da laifukan ƙasa da ƙasa, shige da fice da kuma tabbatar da tsaro. Ta buƙaci a gina dangantaka tsakanin ƙasashen biyu bisa hujjoji da mutunta juna, ba tare da amfani da kalaman siyasa marasa tushe ba.
Shugabar ta kuma yi nuni da nasarorin da gwamnatin Mexico ta samu wajen kama shugabannin ƙungiyoyin cartels, ƙwace miyagun ƙwayoyi da kuma aiwatar da shirye-shiryen tsaro tare da Amurka, tana mai cewa waɗannan matakai sun nuna ƙudirin gwamnatin ta na murƙushe ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Wannan takaddama na ƙara shiga cikin jerin batutuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Mexico da Amurka, musamman kan tsaron iyakoki, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.