Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta zargi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da karya sharuddan da kotu ta gindaya masa na fita domin duba lafiyarsa yayin da yake tsare a hannunta.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar, ICPC ta ce El-Rufai ya ƙi zuwa kotu a ranar farko ta shari'arsa, yana mai neman ganin likitansa na kashin kansa, Farfesa Bello Abubakar.
Hukumar ta ce bayan kotu ta amince da ziyarar jinyar, jami'anta sun raka shi zuwa wani sashe na Asibitin Ƙasa da ke Abuja. Sai dai daga baya ta gano hotuna da aka wallafa a Facebook da ke nuna El-Rufai tare da wasu baƙi, ciki har da ɗan siyasa Isa Ashiru Kudan da kuma likitansa, lamarin da ta ce ya saɓa wa manufar ziyarar jinyar da kotu ta amince da ita.
ICPC ta ce za ta sanar da kotu game da abin da ta bayyana a matsayin karya umarnin kotu, tare da bayyana cewa ta kama Farfesa Bello Abubakar bisa zargin bayar da bayanan ƙarya, kuma ana ci gaba da bincike a kansa.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da mutunta doka, amma ba za ta lamunci amfani da sassaucin da take yi ta hanyar da ba ta dace ba.
