Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buɗe shafin yanar gizo na karɓar sakonnin daukar ma’aikata na shekarar 2026, inda ta gayyaci ‘yan Najeriya masu cancanta su nemi guraben aiki na matakan albashi GL 07, GL 08, GL 09, GL 10 da GL 12.
A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon hukumar, an buɗe shafin karɓar aikace-aikacen ne ranar Litinin, 20 ga Yuli, kuma za a rufe shi ranar Litinin, 27 ga Yuli.
INEC ta bayyana cewa ɗaukar ma’aikatan na da nufin ƙarfafa ƙarfin hukumar wajen gudanar da zaɓe, rajistar masu kaɗa ƙuri’a, sarrafa bayanai da kuma shirye-shiryen kayan zaɓe domin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata.
Hukumar ta ce masu neman aikin za su cike fom ɗin aikace-aikace ta hanyar shafin ɗaukar ma’aikatan INEC, inda za su buɗe asusu, su cike bayanansu sannan su ɗora takardun shaidun da ake buƙata.
INEC ta jaddada cewa neman aikin ba ya buƙatar biyan kuɗi, tare da gargadin masu neman aikin da kada su gabatar da bayanan ƙarya ko takardun bogi, domin duk wanda aka kama da hakan za a soke aikace-aikacensa kuma yana iya fuskantar hukunci a kotu.
Ga guraben da ke buƙatar digiri, masu nema dole ne su mallaki digirin farko ko makamancinsa daga jami’a ko cibiyar da gwamnati ta amince da ita. Inda ya dace kuma, ana buƙatar digirin digirgir (Master’s Degree) a fannin da ya dace.
Haka kuma, dole ne su mallaki takardun shaidar ƙwararru kamar NBA, COREN, NSE, NIQS, ICAN, ANAN ko CPN, su kasance da aƙalla shekara biyu na ƙwarewar aiki bayan kammala karatu, su gabatar da takardar kammala bautar ƙasa (NYSC) ko ta keɓewa, tare da nuna ƙwarewa a fannin nazari, sadarwa, warware matsaloli da amfani da fasahar sadarwa (ICT).
Masu neman wasu guraben kuma dole ne su mallaki Digirin Farko, Higher National Diploma (HND) ko makamancinsa a fannonin Kimiyyar Zamantakewa, Ilimin Dan Adam ko Kimiyya daga cibiyar da aka amince da ita. Haka kuma, ana buƙatar su gabatar da takardar NYSC ta kammala hidima, keɓewa ko wucewa, tare da ƙwarewa wajen sarrafa bayanai, adana bayanai da amfani da shirye-shiryen Microsoft Office da sauran kayan aikin ICT.
Ga masu neman guraben da ke buƙatar NCE, dole ne su mallaki National Certificate in Education (NCE) ko makamancinsa daga cibiyar da gwamnati ta amince da ita, tare da ƙwarewa wajen amfani da kwamfuta, sarrafa bayanai, sadarwa da gudanar da ayyukan ofis.
Yadda ake neman aikin:
- Ziyarci shafin ɗaukar ma’aikata na INEC.
- Buɗe asusun mai neman aiki da cikakkun bayananka, adireshin imel da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN).
- Tabbatar da adireshin imel ɗinka.
- Shiga cikin asusun ka, sannan ka zaɓi matakin aikin da kake son nema.
- Ɗora duk takardun da ake buƙata, ciki har da hoton fasfo, takardar haihuwa ko rantsuwar bayyana shekaru, sakamakon O’Level, takardar Digiri/HND/ND/NCE, takardar shaidar ƙaramar hukuma da takardar NYSC idan ta dace.
- Duba bayanan da ka cike, sannan ka tura aikace-aikacen ta yanar gizo.
Hukumar ta kuma bayyana cewa da zarar an zaɓi wani gurbin aiki, ba za a iya sauya shi ba.
A ƙarshe, INEC ta ce waɗanda kawai aka tantance kuma suka cancanta ne za a gayyata zuwa mataki na gaba na ɗaukar ma’aikatan.