Mutum ɗaya ya rasu yayin da wasu da dama su ka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji kimanin 40, mafi yawansu mata da yara, ya kife a ƙauyen Malamawa da ke gundumar 'Yan Dutse a ƙaramar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Jami'in hulɗa da jama'a na Rundunar 'Yan Sandan Jigawa, SP Shi'isu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an gano gawar mutum ɗaya, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman sauran fasinjojin da suka ɓace.
Ya ce jami'an tsaro, masu aikin ceto da kuma masu sa kai na ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda har yanzu ba a san inda suke ba.
Haka kuma, Masarautar Ringim ta tabbatar da faruwar hatsarin, tana mai cewa ya yi sanadin rasa rayuka, sai dai ba a tantance adadin waɗanda suka mutu da waɗanda aka ceto ba.
A halin yanzu, ana ci gaba da aikin ceto, yayin da hukumomi ke binciken musabbabin hatsarin.
