Mahukuntan Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi (Kogi State Polytechnic), Lokoja, sun dakatar da malamai shida bisa zargin sayar da handout da littattafai ba tare da izini ba, yayin da aka kuma dakatar da wani malami guda bisa zargin cin zarafin ɗaliba ta hanyar lalata, yayin da ake gudanar da bincike kan zarge-zargen neman lalata domin ba da maki, harkokin ƙungiyoyin asiri da sauran laifukan rashin ɗa'a.
Mai magana da yawun kwalejin, John Onimisi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Lokoja.
Sanarwar ta ce an dakatar da malamai shida a ranar Laraba, 22 ga Yuli, 2026, saboda zargin sayar da handout da littattafai ba tare da amincewar hukuma ba, yayin da aka kuma dakatar da wani malami saboda zargin cin zarafin ɗaliba ta hanyar lalata.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan zarge-zargen cin zarafin ɗalibai ta hanyar lalata, ayyukan ƙungiyoyin asiri da sauran nau'o'in rashin ɗa'a a cikin makarantar.
Wasu majiyoyi daga cikin kwalejin sun yi zargin cewa wasu malamai na neman lalata ko kuɗi daga ɗalibai mata domin ba su maki na cin jarabawa. Haka kuma, sun ce ayyukan ƙungiyoyin asiri sun sake bayyana a harabar makarantar.
Wata majiya ta ce matakan ladabtarwa da gwamnatin da ta gabata ta kafa sun yi rauni, lamarin da ya ƙara wa wasu malamai da ɗalibai masu aikata laifi ƙarfin guiwa.
Majiyar ta kuma yi zargin cewa wasu ɗalibai mata da suka kai rahoton cin zarafi ba su samu cikakken goyon bayan makarantar ba, maimakon haka an yi musu barazana.
Haka kuma, an yi zargin cewa ƙungiyoyin asiri sun koma gudanar da tarurrukan dare a harabar makarantar duk da ƙoƙarin da aka yi a baya na dakile irin waɗannan ayyuka.
Sauran zarge-zargen sun haɗa da dawo da tilasta sayen handout, sassauta dokokin sanya kayan ɗalibai da kuma rage tsauraran matakan amfani da katin shaidar ɗalibai, abubuwan da aka ce sun taimaka wajen raguwar ladabtarwa a makarantar.
Da yake mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge, John Onimisi ya ce mahukuntan makarantar sun riga sun miƙa batun ga kwamitin ladabtarwa domin gudanar da cikakken bincike.
Ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin da ya dace bayan an kammala binciken, tare da bayyana sakamakon ga manema labarai a lokacin da ya dace.