Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma mutanen da hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan suka shafa a Jihar Zamfara. Haka kuma, ya umarci rundunar sojoji da ta ƙara ƙaimi wajen ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda a dukkan yankunan Arewa maso Matawalle ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Bungudu da sauran al’ummomin da hare-haren suka rutsa da su, bayan sabon farmakin da ’yan ta’adda suka kai a yankin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar a ranar Lahadi, Matawalle ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na dawo da cikakken zaman lafiya da ƙarfafa tsaro, duk da ƙaruwar hare-haren ta’addanci da ake fuskanta a wasu sassan Arewa maso Yamma.
Ya umarci shugabannin Operation Fansan Yamma da su ci gaba da nuna jajircewa tare da ƙara zafafa kai hare-hare kan ’yan ta’adda, cikin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a yankunan da abin ya shafa.
Bugu da ƙari, ministan ya ba da umarni ga rundunar Operation Fansan Yamma da dukkan rundunonin soji da ke gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci a jihohin Zamfara, Kebbi, Katsina, Sakkwato da Kaduna da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukansu, tare da amfani da dukkan hanyoyin da doka ta amince da su domin murƙushe ayyukan ’yan ta’adda ta hanyar kai hare-haren soji da aka tsara cikin hikima.
Sanarwar ta ce Matawalle ya kuma yi kira ga al’umma, musamman sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, da su ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro ta hanyar ba su ingantattun bayanan sirri cikin lokaci kan mutanen da ke haɗa kai da ’yan ta’adda ko kuma ke ba su bayanan da suke amfani da su wajen kai hare-hare kan ƙauyuka.
Har ila yau, ya umarci manyan kwamandojin sojoji da ke yankunan da matsalar tsaro ta fi ƙamari da su ƙarfafa sa ido tare da ƙara yawan sintiri domin gano da lalata maboyar ’yan ta’adda, sansanoninsu da wuraren da suke fakewa kafin su sake amfani da su wajen shirya ko kaddamar da wasu hare-hare.
Matawalle ya yaba da jarumtaka, ƙwarewa da sadaukarwar dakarun Rundunar Sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro, yana mai jinjinawa nasarorin da suka samu a baya-bayan nan wajen hallaka manyan da ƙananan jagororin ’yan ta’adda a yankunan Gummi, Bukkuyum, Anka, Tsafe, Faskari da sauran wurare.
A ƙarshe, ya buƙaci dakarun tsaron da su ci gaba da wannan ƙwazo tare da ƙara matsa wa ’yan ta’adda lamba har sai an kawo ƙarshen ta’addanci baki ɗaya a dukkan yankunan da abin ya shafa a faɗin Najeriya.