Rundunar Sojin Nijeriya Na Neman Jami'inta Ruwa A Jallo Bisa Zargin Sayar Wa Yan Ta'adda Kaki

Rundunar sojoji ta Nigerian Army Ordnance Corps (NAOC) ta ayyana wani jami'inta mai suna Mohammed Amutu a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zarginsa da sayar da kayan sojoji, musamman kakin soja, ga 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka.

Mohammed Amutu

A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Oluwatope Aluko, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce binciken farko ya nuna cewa Amutu, wanda ke aiki a kamfanin samar da kakin soja na Nigerian Army Ordnance Kits Factory, ya tsere daga sansaninsa tun ranar 3 ga Yuni.

Sanarwar ta ce hukumomin soja sun ayyana shi a matsayin wanda ake nema, tare da ƙaddamar da bincike da farautar sa domin kama shi da gurfanar da shi bisa dokokin soja.

Rundunar ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau'in rashin da'a ko halin da zai iya kawo cikas ga ayyukan tsaro ko barazana ga tsaron ƙasa ba.

Ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani jami'in da aka samu da hannu wajen sayarwa, karkatarwa ko bai wa 'yan ta'adda da masu laifi kayan sojoji ba tare da izini ba, zai fuskanci hukunci mai tsauri bisa dokokin soja da na farar hula.

NAOC ta buƙaci al'umma su bai wa jami'an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen cafke wanda ake nema, tana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin sa ido da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Post a Comment

Previous Post Next Post