Uba Sani Ya Bukaci Mutanen Kaduna Da Su Sake Zaben Tinubu A Karo Na Biyu

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya buƙaci al'ummar jihar su ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu kashi 98 cikin 100 na ƙuri'unsu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, domin nuna godiya bisa ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a jihar.

Uba Sani

Uba Sani ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da ayyukan tituna guda 11 a ƙananan hukumomin Zariya da Sabon Gari. Ya ce gwamnatin Tinubu ta tallafa wa manyan ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa a Kaduna, tare da amincewa da aikin jirgin ƙasa na cikin birni (Light Rail) mai darajar tiriliyan N1, wanda ya ce za a fara aiwatar da shi cikin watanni biyu masu zuwa.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a fara aikin titin Mando zuwa Birnin Gwari cikin mako guda, yana mai cewa shugaban ƙasa ya riga ya fitar da sama da biliyan N100 domin aikin.

Ya ce gwamnatinsa ta ƙaddamar da ayyukan tituna 150 masu tsawon fiye da kilomita 1,355, inda yawancinsu aka kammala, yayin da sabbin titunan da aka ƙaddamar za a gama su cikin watanni biyar.

A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya yabawa Tinubu kan yadda yake zuba jari a fannin ilimi da ababen more rayuwa a Kaduna, yana mai cewa hakan zai ƙara yawan jami'o'in gwamnatin tarayya a jihar zuwa biyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post