Rundunar 'yansandan Jihar Bayelsa ta kama wasu ma'aikatan gwamnati uku bisa zargin hada baki wajen satar kayan gwamnati da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 500.
Kakakin rundunar, Musa Mohammed, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa ana zargin mutanen uku da sace kayayyakin da ke mallakin ma'aikatar kwadago, ci gaban matasa da samar da ayyukan yi ta jihar.
A cewarsa, kayayyakin da aka sace sun haɗa da janareta mai ƙarfin 110 KVA Perkins, motar ɗaga kaya (forklift), injinan lathe, injinan cika kayayyaki da lantarki da wasu kayan aiki masu daraja.
Mohammed ya ce an fara binciken ne bayan an miƙa koke ga Kwamishinan 'yananda, bayan da jami'an ma'aikatar suka gano ɓacewar wasu kayan gwamnati yayin binciken da suka gudanar a ranar 22 ga Yuni.
Ya bayyana cewa tawagar binciken, tare da jami'an ma'aikatar da shugaban sashen kula da ma'aikata, sun duba ɗakin ajiyar kayan aiki da ke harabar Ma'aikatar Sufuri a Yenagoa, inda suka gano cewa wasu muhimman kayayyaki sun ɓace.
Bayan samun rahoton, Kwamishinan 'yansandan jihar ya umarci sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ya gudanar da bincike cikin sirri.
Binciken ya kai ga cafke Wadi Igiran mai shekaru 51 daga yankin Besine a ƙaramar hukumar Yenagoa, Nikade Sunday mai shekaru 59 daga Agbere a ƙaramar hukumar Sagbama, da Azabia Yakie mai shekaru 59 daga Okutukutu a Yenagoa.
Kakakin rundunar ya ce dukkansu ma'aikatan ma'aikatar ne, kuma sun amsa zargin da ake musu.
Mohammed ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
