Zakaran ƙasar Sifaniya, Barcelona, ta soke wasan sada zumunta da ta shirya bugawa da ƙungiyar Ittihad Riadi Tangier ta ƙasar Morocco saboda damuwa kan rikicin iyaka da ke ci gaba da ƙamari a yankin Ceuta.
An tsara wasan ne da za a buga a birnin Tangier ranar 15 ga Agusta, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen Barcelona kafin fara sabon kakar wasa, amma ƙungiyar ta sanar da cewa ba za a ci gaba da wasan ba.
Barcelona ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne saboda rashin tabbas da ke tattare da halin da ake ciki a halin yanzu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce:
“Bisa la’akari da rashin tabbas da kuma yanayin da ake ciki a halin yanzu, FC Barcelona na ganin cewa bai dace a buga wannan wasan ba.”
Ko da yake ƙungiyar ba ta fayyace takamaiman dalilin soke wasan ba, rahotanni sun nuna cewa matakin yana da alaƙa da rikicin da ke ci gaba da faruwa a yankin Ceuta, wani yanki na Sifaniya da ke gabar Arewacin Afirka kuma yake iyaka da ƙasar Morocco.
Lamarin da ke faruwa a Ceuta ya jawo hankalin ƙasashen duniya bayan ƙaruwa da aka samu na baƙin haure da ke ketarowa daga Morocco zuwa yankin na Sifaniya, lamarin da ya haifar da matsalolin diflomasiyya da tsaro ga wasu ƙasashen Turai.
Dubban baƙin haure sun shiga yankin Ceuta, inda hukumomi ke ci gaba da kokarin shawo kan matsalolin jin ƙai da kuma na kula da iyakoki. Duk da cewa an mayar da da dama daga cikinsu zuwa Morocco, har yanzu dubban mutane na ci gaba da zama a Ceuta.
Soke wasan ya ƙara jefa cikas ga shirye-shiryen Barcelona na kafin fara kakar wasa. A baya ma an soke wani wasan sada zumunta da ƙungiyar Preston North End bayan sansanin horon da Barcelona ta yi a Birtaniya, inda ta buga wasa da Birmingham City.
Ana sa ran Barcelona za ta ci gaba da shirye-shiryenta ta hanyar wasannin sada zumunta masu zuwa, ciki har da karawa da Nottingham Forest a birnin Udine na ƙasar Italiya, da kuma wasa da ƙungiyar Al Ahly ta Masar ranar 19 ga Agusta.
Ƙungiyar da koci Hansi Flick ke jagoranta za ta fara kare kambunta na La Liga ranar 23 ga Agusta da wasa da Elche, inda take fatan fara sabon kakar wasa da ƙarfi.