Gwamnan Enugu ya ware Fili Domin gina Cobiyar Kera Kayayyakin Dijital ta Zamani

Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya amince da ware wani fili a birnin Enugu, babban birnin jihar, domin kafa wata cibiyar ƙera kayayyakin dijital ta zamani (Digital Fabrication Centre) da Asusun Horar da Ma’aikata na Ƙasa (Industrial Training Fund – ITF) zai gina.

Mbah ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga ITF da ta kai masa ziyarar girmamawa a Fadar Gwamnatin Jihar Enugu.

ITF ta sanar da hakan ne a ranar Juma’a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Thomas Ngor, ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, gwamnan ya bayyana cewa aikin da ake shirin yi ya zo a kan lokaci kuma ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta mayar da Enugu ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin zuba jari, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa masana’antu masu amfani da fasaha.

Ya ce makomar bunƙasar tattalin arziki tana cikin zuba jari da gangan a fannin haɓaka ƙarfin ɗan Adam da kuma sabbin fasahohi. Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da ci gaba mai ɗorewa.

Mbah ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sanya ilimin fasaha ya zama wajibi a makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare na jihar, tare da mai da hankali kan ilimin dijital, robotics da mechatronics, domin shirya ɗalibai da matasa domin ayyukan nan gaba.

A cewarsa, yawancin sana’o’in gargajiya a yau suna gudana ne ta hanyar amfani da fasahar dijital, don haka ya zama dole a ba matasa ƙwarewar fasaha da za ta ba su damar yin gogayya a matakin duniya tare da bayar da gudunmawa ga bunƙasar tattalin arziki.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina makarantun zamani (smart schools) a faɗin jihar, tare da tanadar cibiyoyin robotics, dakunan gwaje-gwajen mechatronics da sauran kayayyakin koyarwa na zamani domin shirya matasa ga sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.

Ya kuma yi nuni da cewa ana sa ran fasahar basirar wucin gadi (Artificial Intelligence – AI) za ta ba da gudunmawar kusan dala tiriliyan 20 ga tattalin arzikin duniya cikin shekaru masu zuwa. 

Post a Comment

Previous Post Next Post