Daraktan NYSC ya Yaba da Yadda Aka Gyara Sansanin Horaswa na Abiya


Daraktan Janar na Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aikin gyaran sansanin horaswa na NYSC da ke Jihar Abiya ke gudana, yana mai cewa sansanin ya samu gagarumin sauyi idan aka kwatanta da yadda ya same shi a ziyararsa ta baya.

Nafiu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima na rukunin 2026 Batch B Stream 2 da ke Umunna, a ƙaramar hukumar Bende.

Ya ce an kammala mataki na farko na aikin gyaran sansanin, yayin da ake jiran fara aiwatar da mataki na biyu.

“Na zo domin na gani da idona yadda atisayen horaswa na 2026 Batch B Stream 2 ke gudana. A ziyarata ta baya, gine-gine da kayan more rayuwa na sansanin sun kasance cikin mummunan hali. Amma yanzu, aƙalla an kammala mataki na farko na aikin gyaran,” in ji shi.

Daraktan Janar ya ce masu yi wa ƙasa hidima da aka tura Jihar Abiya suna bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziki da ci gaban jihar, musamman a fannonin lafiya, ilimi da injiniya.

“Waɗannan matasa sun zo ne domin yi wa ƙasa hidima. Sun zo ne domin haɗa kan al’umma da ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomi. Haka kuma suna koyon al’adun mutanen Jihar Abiya,” in ji shi.

Nafiu ya bayyana cewa a halin yanzu akwai likitoci sama da 53 da ma’aikatan jinya 112 da ke gudanar da hidimar ƙasa a jihar, baya ga malamai da injiniyoyi.

Ya ƙara da cewa, “Za su koyi al’adun mutanen jihar, za su koma gida da abubuwan alheri da suka koya, kuma za su taimaka wajen ci gaban Jihar Abiya.”

Ya shawarci masu yi wa ƙasa hidima da su kasance jakadu nagari ta hanyar mutunta al’adu da ƙimomin mutanen Abiya. Haka kuma ya roƙi al’ummar jihar da su karɓe su hannu bibbiyu.

“Saƙona gare su shi ne su kasance baƙi na gari, su mutunta al’adu da ƙimomin mutanen Jihar Abiya. Ina kuma roƙon mutanen jihar da su ɗauke su a matsayin ’ya’yansu da ’yan’uwansu, su tarbe su da hannu bibbiyu,” in ji shi.

Nafiu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin NYSC da gwamnatin jihar domin a cimma cikakkiyar fa’idar shirin.

Dangane da ƙarin tallafin da ake buƙata daga gwamnatin jihar, ya ce zai gabatar da wasu buƙatu yayin ganawarsa da Gwamnan Jihar Abiya.

“Mai Girma Gwamna ya amince da ba ni damar ganawa da shi. Daga nan zan je in tattauna da shi tare da gabatar masa da wasu ƙarin buƙatu. Ya nuna kyakkyawar haɗin kai, amma za mu ci gaba da tattaunawa,” in ji shi.

A nasa jawabin, Kodinetan NYSC na Jihar Abiya, Mista Yunusa Tanimu, ya bayyana cewa masu yi wa ƙasa hidima 1,753 ne suka yi rajista domin wannan atisayen horaswa, ciki har da maza 760 da mata 993.

Ya ce matasan da aka tura jihar suna da ɗa’a, ƙwazo da kuma iya daidaitawa da tsarin rayuwar sansanin.

Tanimu ya bayyana cewa dukkan ayyukan sansanin, da suka haɗa da laccoci, atisayen fareti, dabarun soja, wasanni, nishaɗi da shirin Samar da Ƙwarewa da Harkokin Kasuwanci (SAED), suna gudana cikin nasara, tare da cikakken halartar masu yi wa ƙasa hidima.

Ya ƙara da cewa asibitin sansanin na samun kulawa daga likitoci 12, ma’aikatan jinya 19, masu hada magunguna 13 da sauran ma’aikatan lafiya 21, tare da haɗin gwiwar wani likita da wata ma’aikaciyar jinya daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Umuahia.

Kodinetan ya ce tsaro a cikin sansanin da kewaye da shi ya kasance cikin kwanciyar hankali, yana mai cewa NYSC na aiki tare da hukumomin tsaro da jami’an tabbatar da doka domin ƙarfafa tattara bayanan sirri, kula da hanyoyin shiga da kuma inganta tsaro gaba ɗaya.

Da yake bayyana wasu nasarorin da aka samu tun bayan hawansa ofis, Tanimu ya ce an sayo kujeru roba 251 a lokacin atisayen horaswa na 2026 Batch B, yayin da aka ƙara sayo kujeru 110 domin atisayen da ake gudanarwa yanzu.

Ya kuma ce an yi wa ƙofar shiga sansanin da bangon wajen sansanin fenti tare da rubuce-rubucen NYSC, sannan an gina hanyar hawa ta musamman (ramp) zuwa dandalin babban zauren taro domin bai wa masu amfani da keken guragu damar isa dandalin cikin sauƙi, daidai da manufar hukumar ta tabbatar da bai wa kowa dama.

Post a Comment

Previous Post Next Post