Shahararren mawakin Afrobeats na Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya roƙi Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya sanya ido kan damuwar da ake da ita game da zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa.
Davido ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana fargabar yiwuwar barkewar tashin hankali, amfani da barazana da kuma kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya a jihar.
Mawakin ya bukaci Trump da sauran ƙasashen duniya su sanya ido sosai kan zaben, tare da ƙarfafa hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da tsaron masu zaɓe da kuma mutunta kuri’ar kowane ɗan ƙasa.
Davido ya ce al’ummar Osun na da hakkin yin amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki wajen zaɓe cikin ’yanci da lumana, ba tare da tsoro ba.
Ya kuma yi kira da a gudanar da zaben cikin lumana, gaskiya da sahihanci, ba tare da tashin hankali ko tsoratarwa ba.
