Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa EFCC Reshen Jihar Kano Ta Kaddamar Da Binciken Wani Matashi Haruna Yusuf Bisa Zargin Shigowa Da Wasu Makudan Kudaden Waje Ba Bisa Ka'ida Ba

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya, EFCC, reshen Jihar Kano, ta ƙaddamar da binciken wani mutum mai suna Haruna Yusuf, jin kaɗan bayan Hukumar Kwastam ta ƙasa ta kama wasu maƙudan kuɗaɗen ƙasashen waje da ba a bayyana masu su ba a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano (MAKIA).

Kuɗaɗen da aka kama sun haɗa da: dalar Amurka dubu $73,000, da fam ɗin Birtaniya £15,957 da kuma Riyal ɗin Saudiyya 827,800 a cikin jakar.

Hukumar Kwastam ta ƙasa  ta ce jami’anta sun kama kuɗaɗen ne a lokuta biyu mabambanta, tsakanin ranar Asabar 8 da kuma ranar Laraba 12 ga Agusta 2026, a lokacin da suke gudanar da binciken fasinjoji da kayayyakin da suke shigowa da su ƙasar.

A ranar Addabar  8 ga Agusta, jami’an Kwastam sun kama Riyal 827,800 da dalar Amurka $53,300 a cikin wata jaka da ta shigo daga jirgin Saudi Air, inda aka ɓoye kuɗaɗen cikin takalma.

Sai kuma ranar Laraba 12 ga Agusta, inda jami’an Kwastam ɗin suka tsayar da wata jaka mallakin wani mutum da ake kira Haruna Yusuf, wanda ya iso Kano daga cikin jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET941.

Binciken da aka gudanar ta amfani da na’urar Non-Intrusive Inspection Technology ya gano dala $20,000 da Riyal £15,957, waɗanda aka ɓoye cikin takalman wasanni nasa ne.

Mukaddashin Kwanturolan Yankin Kwastam na Kano/Jigawa, U.U. Adamu, ya miƙa wanda ake zargin da kuɗaɗen ga EFCC domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi gaban ƙuliya, idan har aka samu gamsassun hujjojin aikata laifi.

A nasa jawabin, Muƙaddashin Daraktan EFCC na Shiyyar Kano, Friday S. Ebelo, ya yaba wa Hukumar Kwastam bisa haɗin gwiwa da ƙwarewar da jami’anta suka nuna wajen gano kuɗaɗen.

Ebelo ya yi kira ga matafiya da su riƙa bayyana adadin kuɗaɗen ƙasashen waje da suke ɗauke da su yayin shigowa ko fita daga Nijeriya, yana mai cewa rashin bayyana makudan kuɗaɗe ya saɓa wa dokar hana safarar kuɗaɗen haram ta shekarar 2022.

Post a Comment

Previous Post Next Post