Ministan Abuja, Nyesom Wike Ya Bayar Da Umarnin Rushe Duk Wani Gida Da Aka Yi Shi a Kan Hanyar Ruwa; Ko da Kuwa Gidan Minista Ne.

Ministan Abuja Nyesom Wike ya ba da umarnin rushe gidajen da suke toshe magudanan ruwa a cikin birnin Abuja

Ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya bayar da umarnin a fara rushe gidajen da ke toshe hanyoyin magudanan ruwa a unguwannin Maitama da sauran wuraren da ke fama da ambaliyar ruwa a Abuja.

Ministan ya bayar da umarnin ne ranar Talata18 ga Agusta 2026, bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama.

Ya ƙara da cewa, rushe-rushen za su fara ne nan take, kuma za a ci gaba da rushe duk gidan da yake a kan hanyar ruwa daga nan har zuwa ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026 ba tare da la’akari da harkokin siyasa ko matsayin masu mallakar gidajen ba.

Wike ya ce ɗaukar wannan matakin ya zama dole ne, domin ƙoƙarin kawar da abubuwan da suke hana kwararar ruwa da kuma rage barazanar ambaliyar ruwa a Abuja.

Ministan ya ɗauki wannan matakin ne, jin kaɗan bayan wata ambaliyar ruwa da ta auku a cikin babban birnin tarayyar na Nijeriya, wanda ya haifar da cece-ku-ce sosai a cikin al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post