Isra’ila ta ƙara tsawaita matakan da take ɗauka kan Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da agaji ga Falasɗinawa (UNRWA), yayin da ake zargin cewa matakan na da alaƙa da ƙoƙarin ci gaba da shirin mamaye wasu sassan Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Hukumomin Isra’ila sun ɗauki matakai da dama na takaita ayyukan UNRWA, suna zargin hukumar da kasancewa da alaƙa da wasu masu fafutukar Falasɗinawa. UNRWA ta musanta zarge-zargen da ke cewa tana tallafa wa ayyukan mayakan Falasɗinawa, tana mai cewa aikinta na mayar da hankali ne kan samar da agaji, ilimi da kiwon lafiya ga Falasɗinawa.
Masu sukar manufofin Isra’ila sun ce raunana ko dakatar da ayyukan UNRWA na iya ƙara wahalar da rayuwar Falasɗinawa, musamman a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, magunguna da sauran muhimman kayan agaji.
Wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa da masu sa ido na ƙasa da ƙasa suna ganin cewa takaita ayyukan UNRWA na iya kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin sauya yanayin demografiya da siyasar Gabar Yamma, musamman yayin da wasu jami’an Isra’ila ke ci gaba da nuna goyon baya ga faɗaɗa matsugunan Yahudawa da kuma mamaye ƙarin filayen Falasɗinawa.
Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin jin ƙai sun yi gargaɗin cewa duk wani mataki da zai hana isar da agaji ga fararen hula na iya ƙara tsananta matsalar jin ƙai da ake fuskanta a yankunan Falasɗinawa.