Wata rana Kura 🐆ta yi wa wani Zaki 🦁laifi sai ta gudu. Zaki ya shiga neman Kura, ya yi duk kokarinsa amma bai samu damar kama kura ba, sun sha haduwa amma Kura ba ta kamu ba, saboda shegen gudun tsiya. Da Zaki ya rasa yadda zaiyi sai ya tabbatar idan ba da dabara ba, Kura ba za ta taba kamuwa ba.
Don haka Zaki ya shirya wata dabara, sai yaje ya kamo Akuya,🐐sai Akuya ta kama kuka da ihu, ta na cewa zaki laifin me nayi maka? Don Allah ka kyale ni, sai Zaki yace bakiyi min laifin komai ba, kuma ba wani abu zanyi miki ba. So nake na labe a jikin bishiyar nan! Ga kura can ta taho, idan ta iso abinda nake so shi ne ki zage ta, so nake na kamata.
Shi ke nan Akuya ta kwantar da hankalinta, ta zauna a gindin bishiyar, shi kuma Zaki ya labe a bayan bishiyar.
Can sai ga Kura ta tinkaro wajen bishiyar, amma ba ta lura akwai Akuya a gindin bishiyar ba, tazo zata wuce, sai Akuya tace KE KURA UWAKI!!! Sai Kura ta waigo tace Akuya ni kike Zagi?, sai Akuya tace an zageki din dan ubanki kiyi abinda zakiyi.
Sai Kura ta fusata ta yiwo kan Akuya a fusace zata yagalgalata, can sai Kura ta tsaya tayi tunani ta ce kai jama'a! Abin da zai sa haka kawai da rana tsaka Akuya ta zageni ba karami abu bane! lalle da akwai wani abu da ta taka, ko kuma a akwai wani abu shiryayye, sai Kura ta fasa ta gyada kai tayi tafiyarta har da hadawa da gudu-gudu.
