2027: Allah Ne Kadai Zai Iya Hana Tinubu Sake Lashe Zabe - Datti

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya ce Allah ne kaɗai zai iya hana Shugaba Bola Tinubu sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Datti

Datti ya bayyana haka ne a wata hira da TrustTV, inda ya ce duk da cewa bai amince da wasu manufofin Tinubu ba, yana ganin shugaban ya yi ƙoƙari wajen gina tsarin siyasa da kulla ƙawance na tsawon shekaru.

Ya ce Tinubu ya shafe kusan shekaru 16 yana gina tsarin siyasarsa, tare da taka muhimmiyar rawa wajen haɗa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da wasu ‘yan siyasa kafin zaɓen 2015.

Datti ya kuma bayyana nasarar Tinubu a zaɓen 2023 a matsayin wata babbar nasarar siyasa, yana mai cewa shugaban ya samu gagarumar rinjaye a fagen siyasar ƙasar.

Ya zargi ‘yan adawa da rashin haɗin kai, tare da cewa Tinubu na da matuƙar tasiri a siyasar ƙasar da zai iya hana jam’iyyun adawa haɗa kai.

“Idan Tinubu ya ce wani abu zai faru, Allah Maɗaukaki ne kaɗai zai iya hana shi,” in ji Datti, yayin da yake magana kan yiwuwar Tinubu ya sake samun nasara a 2027.

Datti, wanda ya kasance mataimakin Peter Obi a zaɓen 2023, ya ce a halin yanzu “Najeriya ta zama ta Tinubu”, yana mai barin jama’a su fassara kalaman nasa yadda suka ga dama.

Post a Comment

Previous Post Next Post