Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Amince da Sabon Yarjejeniyar Albashi Tsakaninta FGN da ASUU Domin Malaman KASU


Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da sabuwar yarjejeniyar albashi wanda za ta fara aiwatar da shi daga albashin watan Oktoba 2026; Gwamna Uba Sani ya yi kiran da a kiyaye zaman lafiya tare da haɓaka ingancin karatu.

A wani babban mataki na inganta jin daɗin ma'aikatan ilimin gaba da sakandare, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da yarjejeniyar albashi ta shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (FGN–ASUU) ga malaman Jami'ar Jihar Kaduna (KASU).

Sabuwar yarjejeniyar jin daɗin za ta fara aiki ne a hukumance daga albashin watan Oktoba 2026.

Wannan shawara ta biyo bayan miƙa rahoton kwamitin shawarwari tsakanin Gwamnati, KASU, da ASUU mai mambobi 9 da Gwamna Sani ya kafa domin duba buƙatun ƙungiyar da kuma samar da tsari mai ɗorewa. A ƙarƙashin sabon tsarin da aka amince da shi, malaman KASU za su amfana da sabuntawar tsarin albashin CONUASS da tallafin kayan aikin karatu (CATA), tare da sauran gyare-gyaren albashi da alawus-alawus.

Yayin da yake sanar da amincewar a ranar Juma'a, Kwamishinan Ilimi kuma Shugaban Kwamitin Shawarwarin, Prof. Abubakar Sani Sambo, ya bayyana cewa wannan mataki yana nuna ci gaba da ba da muhimmanci ga bunƙasa albarkatun jama'a.

'Gwamnati ta kasance tana ware aƙalla kashi 25 cikin ɗari na kasafin kuɗin jihar na shekara don fannin ilimi,' in ji Prof. Sambo, yayin da yake bayyana nasarorin da jihar ta samu a fannin ilimi.

Tun bayan karɓar mulki a shekarar 2023, gwamnatin ta gina da kuma gyara azuzuwan karatu 3,267, ta samar da bayan gida 1,194 da fanfunan burtsatse 90, sannan ta rarraba kayan zamani 57,777 ga makarantu a faɗin Kaduna.

Sauran matakan sun haɗa da rage kuɗin makarantun gaba da sakandare da kashi 50, ƙara shekarun ritaya na malamai daga 60 zuwa 65, da kuma maido da yara fiye da 300,000 da ba sa zuwa makaranta zuwa ajujuwa daga cikin fiye da 500,000 da aka gada.

Sanarwar ta bayyana cewa sauye-sauyen da Kaduna ta aiwatar bisa ƙwaƙƙwarar shaida sun samu karɓuwa a matakin ƙasa. Gwamnatin Tarayya ta ɗauki tsarin Kaduna na bin sawun yara marasa zuwa makaranta gida-gida a matsayin tsarin ƙasa, yayin da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta buƙaci littattafan horar da sana'o'i na jihar don amfani da su a matsayin jagora a matakin ƙasa.

Bayan yarjejeniyar, gwamnatin jihar ta yi kira ga ƙungiyoyin ma'aikatan jami’ar har da ASUU, SSANU, NASU, da NAAT da su maida martani mai kyau ta hanyar rungumar tattaunawa maimakon yajin aiki.

Haka zalika, gwamnatin ta ƙalubalanci shugabannin KASU da malamanta da su yi amfani da wannan ƙarin jin daɗi wajen inganta binciken ilimi da koyarwa, da kuma ɗaukaka matsayin jami'ar a ma'aunin jami'o'in duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post