Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce mukaman gwamnati suna da matukar muhimmanci, don haka bai kamata a damƙa su ga mutanen da ba sa tsoron Allah ba.
Fayemi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron limaman Cocin Katolika na Najeriya (CBCN) da aka gudanar a Osun.
Ya bukaci mabiya addinin Katolika da kada su janye daga harkokin siyasa, yana mai cewa hakan na iya bai wa “’yan siyasa marasa ka’ida” damar karbe mulki.
A cewarsa, shiga siyasa bai kamata ya takaita ga kada kuri’a kawai ba, sai dai ya haɗa da tsayawa takara, shiga jam’iyyun siyasa, wayar da kan masu kada kuri’a, sanya ido kan zabe da kuma rike zababbun shugabanni da alhaki.
Fayemi ya kuma shawarci Kiristoci da kada su bari kabila, addini, son kai, alfanun kudi ko makauniyar biyayya ga jam’iyya su rinjayi zabinsu a zaben 2027.
Ya ce kamata ya yi a tantance ‘yan takara da manufofinsu bisa yadda za su inganta mutuncin dan Adam, adalci, zaman lafiya, tsaro, ci gaba da moriyar al’umma.
Tsohon ministan ma’adanai ya kuma bukaci Cocin Katolika ta kara horas da matasa kan kundin tsarin mulki, dokokin zabe, shugabanci nagari, kare hakkin dan Adam, sayen kuri’a, rashin fitowa zabe da tashe-tashen hankula a lokacin zabe.
