Iran ta Gargaɗi Jiragen Ruwan Amurka da ke Tunkarar Mashigar Hormuz

Mataimakin kwamandan rundunar sojojin ruwa ta Juyin Juya Halin Iran, Ali Mohammadi, ya yi tsokaci kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump na cewa yana iko da mashigin Hormuz, inda ya ce: “Idan haka ne, da sunan Allah. Ku kawo ɗaya daga cikin jiragen ruwanku cikin tazarar kilomita 100.”Babban jami'in na IRGC ya ce “Amurkawa sun san cewa idan jiragen ruwansu suka kusanto, za su fuskanci martani daga mayaƙan Iran,” sannan ba tare da bayar da cikakken bayani ba, ya yi iƙirarin cewa “an samu irin wannan misali a kwanakin baya.”

Da yake magana a wani taron dare na magoya bayan gwamnati a birnin Mashhad, ya ce: “A yau... babu sojojin Amurka a Tekun Fasha, Tekun Oman da mashigar Hormuz, sannan babu kayan aikin sojin Amurka da aka jibge a waɗannan yankuna. Idan Amurkawa suka kusanci yankin da aka kayyade, su kansu sun san abin da zai faru da su.”

A cewarsa, “duk wani jirgin ruwa da ya taso daga Kuwait ko Bahrain, ba tare da togiya ba, yana ƙarƙashin sa ido na rundunar sojojin ruwa ta IRGC, kuma idan aka gano wani take doka, za a ɗauki mataki a kansa bisa ƙa'idojin da aka tanada.”

Post a Comment

Previous Post Next Post