Fitaccen mawaki kuma ɗan wasan Kannywood, Ado Gwanja, yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
Mawaki Ado ya shafe sama da kwanaki 40 yana jinya, inda rashin lafiyar ta kai wani mataki da yake buƙatar taimako wajen gudanar da wasu abubuwan yau da kullum.
Ya zuwa yanzu an tabbatar mana da cewa an dawo da shi gida domin ci gaba da samun kulawa da jinya. Sai dai, har zuwa yanzu ba'a san musabbabin wannan rashin lafiya tashi ba.
Ado Gwanja ya shahara a masana’antar Kannywood da wakokinsa da kuma salonsa a wasu lokuta ya kasance ana muhawara a kansa daga bangarori daban-daban na al’umma.
A irin wannan lokaci, abin da ya fi dacewa shi ne a yi masa addu’ar samun sauƙi da lafiya.
Wannan ya zama babban darasi ga kowa. Matuƙar kana da dama, kana cikin ƙoshin lafiya kuma kana da ƙarfin yin abin da ya dace, kada ka jinkirta gyara rayuwarka da kusantar Allah.
Rayuwa ba tabbas ce, kuma lafiyar da muke da ita yau babbar ni’ima ce. Abin da mutum zai iya yi cikin sauƙi yau, wata rana yana iya rasa ikon yin sa.
Don haka, mu yi amfani da lokacin da Allah Ya ba mu wajen aikata alheri, gyara halayenmu, nisantar abin da bai dace ba, da kuma neman yardar Allah.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba Ado Gwanja cikakkiyar lafiya, Ya sauƙaƙa masa wannan jarabawa, Ya kuma dawo da shi cikin ƙoshin lafiya.
