Gwamnatin Burtaniya ta ce matakan za su taƙaita damar Iran ta ke da shi na shiga tsarin kuɗi na Burtaniya da kuma faɗaɗa haramcin ciniki zuwa ƙarin wasu kayayyaki da fasahohi da ayyuka.
Matakan za su kuma hana jiragen saman Iran sauka a ƙasar Birtaniya, sai dai a cikin wasu lokutan da aka keɓe.
Stephen Doughty, babban jami'in Ofishin Harkokin Waje na Burtaniya, ya ce a cikin wata sanarwa cewa dokar "ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarinmu na daƙile burin mallakar nukiliya na Iran" kuma za su taimaka wa London wajen tabbatar da cewa Iran ba za ta taɓa samun makaman nukiliya ba.