Kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC), ya ce Iran ta ƙwace wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku na Amurka mai amfani da fasahar zamani da sarrafa kansa.
A cewar Fars, jirgin ruwan na daga cikin sabbin jiragen ruwa marasa matuƙa, masu amfani da fasahar zamani da Amurka ke da su.Kamfanin ya ce an kama jirgin ruwan ne a mashigar Hormuz, muhimmin mashigin ruwa da ke haɗa Tekun Fasha da Tekun Oman.
Ya zuwa yanzu, Amurka ba ta mayar da martani kan wannan rahoto ba.