An Sake Kashe ’Yan Najeriya Biyu a Afirka Ta Kudu

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da mutuwar ’yan Najeriya biyu a wasu hare-hare daban-daban a Afirka ta Kudu, yayin da ake ci gaba da fargabar hare-haren kyamar baki da ake kai wa ’yan kasashen waje.

Afirka

Mai magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Oluwafemi Adeniyi, ya ce an kashe Taiwo Fakunle a gidansa da ke Kensington, Johannesburg, ranar 4 ga Satumba.

Ya ce an kuma kashe James Nwankwo washegari a Somerset, Cape Town, yayin wani bincike da jami’an ’yan sandan Afirka ta Kudu (SAPS) suka gudanar, inda aka zargi jami’an da amfani da hanyoyin tambayoyi masu muni.

Ma’aikatar ta bukaci hukumomin Afirka ta Kudu su gudanar da cikakken bincike kan mutuwar mutanen tare da gurfanar da duk wanda ke da hannu a gaban shari’a.

Gwamnatin Najeriya ta kuma nuna damuwa kan ci gaba da kai hare-hare da lalata kadarorin ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka a kasar.

Lamarin ya zo ne watanni biyu bayan kashe wasu ’yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu.

Gwamnatin ta ce tana duba wasu matakai na diflomasiyya, ciki har da kai batun hare-haren kyamar ’yan Afirka gaban ECOWAS da Tarayyar Afirka (AU).

A gefe guda, Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da dukkanin hulɗar majalisa da Afirka ta Kudu saboda ci gaba da kai wa ’yan Najeriya hare-hare.

Post a Comment

Previous Post Next Post