Akalla fursunoni 23 ne suka mutu a gidajen yarin Tunisia cikin makonnin baya-bayan nan sakamakon tsananin zafi, a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar (LTDH).
Shugaban kungiyar, Bassem Trifi, ya ce sun tattara bayanan mutanen da suka mutu ne daga likitoci, lauyoyi da ‘yan uwansu.
Ya ce yanayin gidajen yarin ya kara tsananta ne saboda cunkoso, rashin isasshen iska da karancin ruwa, yayin da yanayin zafi a wasu lokuta ya haura digiri 45 na ma’aunin Celsius.
Sai dai hukumomin Tunisia ba su fitar da adadin wadanda suka mutu a gidajen yari a lokacin zafin ba, inda wani jami’i ya ce ba za a danganta mutuwar wani da zafi ba sai an tabbatar da hakan daga likitocin binciken gawa.
Kungiyar World Organisation Against Torture (OMCT) ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsare mutane da karuwar mace-mace a gidajen yarin kasar, tare da bukatar gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun kuma bukaci hukumomi su dauki matakan gaggawa domin kare rayukan fursunoni, musamman yayin da ake fama da matsanancin zafi da matsalolin wutar lantarki da ruwa.
