Fim din 1976 na (the Message) ya fuskanci cece-kuce saboda haramcin da Musulunci ya yi a kan siffanta Annabi Muhammadu (SAWW), ko da yake an yi fim ɗin ne don kauce wa hakan ta hanyar rashin nuna shi (ma'ana wani bai taka rawa a fin din da sunansa ba).
Bugu da kari, tun da farko wasu malaman addinin Musulunci masu ra'ayin rikau da masana sun nuna adawa da fim din, har da tsinuwa da kafirta daraktan da ya shirya fim din da duk wani musulmi daya taka rawa a cikinsa, duk da cewa darakta Moustapha Akkad musulmi ne mai kishin addini wanda ya yi nufin sanya fim din a matsayin wata gada ta mutuntawa tsakanin Musulunci da kasashen Yamma.
Suka daga Malamai
Duk da wannan taka-tsantsan da aka yi fim din ya sha suka daga malaman addinin Musulunci masu ra’ayin rikau da masana, wadanda suke ganin har yanzu fim din yana bata sunan addini ko kuma cin mutuncin Musulunci.
Garkuwa Da Mutane A Amurka
A lokacin da aka shirya fara haska fim din a kasar Amurka, wata kungiya ta Hanafiyya ta musulmin kasar, ta yi garkuwa da mutane a birnin Washington DC.
Bukatunsu sun hada da hana nuna fim din, bisa kuskuren cewa jarumin da ya fito a film din Anthony Quinn (wanda ya fito a Sayyidina Hamza AS) ya fito ne a matsayin Annabi Muhammad (SAWW) da kansa.
Garkuwar ta tsawon sa'o'i 39 ta yi sanadin mutuwar wani dan jarida da dan sanda, kuma duk da cewa an dakatar da haska fim din, amma hakan ya janyo mummunan tasiri a kan rashin cinikin film din a Amurka.
Haramtawa
An haramta fim din a wasu kasashen Larabawa da suka hada da Masar, Kuwait, da Saudiyya, saboda bambancin ra'ayi na addini da al'adu.
Canja Sunan Fim Din
An canza sunan daga (Mohammed, Messenger of God) zuwa (the Message) jim kaɗan kafin kaddamar da fim din a London don kauce wa jayayya da barazana.
Nufin Daraktan
Darekta fim din Ba’amurke dan kasar Syria Moustapha Akkad ya shirya fim din the Message da nufin samar da fahimtar juna tsakanin Musulunci da kasashen yamma ta hanyar ba da labarin jarumtaka da sadaukarwar Musulunci.
Gudummawar Muammar Gaddafi
Gwamnatin Muammar Gaddafi ta ba da tallafin kudi ga fim din The Message a shekarar 1976, wanda ke nuna farkon bullar Musulunci da farkon tarihin Musulunci a Makka da Madina. Shirye-shiryen fim din ya tsaya cik saboda matsalar kudi, amma Gaddafi ya bayar da kudade, wanda ya ba da damar kammala aikin. Fim din ya kasance wani fitaccen shiri na al'adu a lokacin mulkin Gaddafi a Libya, wanda galibi ana nunawa a duk shekara a gidan talabijin na gwamnati.
Don Neman Karin Bayani Rubuta The Message faced controversy a kan Google.
