Tsohon Shugaban PDP Kuma Gwamnan Tsohuwar Jihar Gongola Bamanga Tukur Ya Mutu Yana Dan Shekara 90; Tinubu Ya Aika Sakon Ta'aziyya

Tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 90 a duniya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci al'umma wajen miƙa saƙon ta'aziyya a ranar Asabar, inda ya kwatanta mutuwar dattawan ƙasar a matsayin ƙarshen wani muhimmin babi a tarihin siyasa da tattalin arziƙin Najeriya.

A cikin wata sanarwa a hukumance da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Siyasa da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana Tukur, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Tafidan Adamawa, a matsayin "jigo a ƙasa" wanda aikinsa a fannin gwamnati da kasuwanci ya bar gurbi mai zurfi a fannin gudanarwa da masana'antu, da shugabancin da kasuwanci a faɗin Afirka.

"Alhaji Bamanga mutum ne mai mutunci, ma'abocin kyauta da riƙo da gaskiya da hidimta wa al'umma da riƙo da al'adu, mutum ne wanda Masarautar Adamawa da ma ƙasa bakiɗaya ke taƙama da su," in ji Shugaba Tinubu. 

"Mutum ne mai hangen nesa da kwarjini wanda ya amince da ɗimbin damammakin da Najeriya ke da su. Lallai Najeriya za ta yi rashin shawarwarinsa na hikima da babban shugabanci na uba kuma jagora."

An haifi Bamanga a ranar 15 ga Satumba, 1935, Alhaji Tukur ya fito fili a matsayin Babban Manaja na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) daga shekarar 1975 zuwa 1982, inda ya jagoranci muhimman sauye-sauye wajen zamanantar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa da inganta harkokin ruwa na Najeriya.

Daga bisani ya shiga harkokin siyasa gadan-gadan a Jamhuriyya ta Biyu, inda ya lashe zaɓen Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola a shekarar 1983, yankin da a yanzu ya haɗa da Jihohin Adamawa da Taraba.

Bayan zamansa a gwamnan jiha, Tukur ya fice a matsayin sanannen ɗan kasuwa, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kamfanonin BHI Holdings da DADDO Group of Companies, waɗanda ke gudanar da ayyuka a fannin masana'antun: noma da sarrafa kayayyaki da kasuwancin ƙasa da ƙasa. Daga baya ya koma harkar gwamnati a matsayin Ministan Masana'antu na Ƙasa a ƙarƙashin gwamnatin Janar Sani Abacha daga shekarar 1993 zuwa 1995.

Kasancewarsa zakaran gwajin dafi wajen haɗin kan tattalin arziƙin Afirka, an girmama Tukur a faɗin nahiyar saboda aikinsa a matsayin Shugaba  a Babban Taron Kasuwancin Afirka (African Business Roundtable) da Shugaban Ƙungiyar Kasuwanci ta NEPAD, inda ya jagoranci fafutukar bunƙasa kasuwancin masu zaman kansu da faɗaɗa kasuwanci a tsakanin ƙasashen Afirka.

A fannin shugabancin siyasa, Bamanga ya yi aiki a matsayin Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa daga Maris 2012 zuwa Janairu 2014, zamanin da Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya ba da gudummawa mai tarin yawa ga tsarin dimokuraɗiyyar ta hanyar tabbatar da horo a jam'iyya da samar da daidaito.

Shugaba Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa zuwa ga iyalan Bamanga da Masarautar Fombina ta Adamawa, Gwamnati da al'ummar Jihar Adamawa, da kuma abokan hulɗar Tukur a fannin kasuwanci da siyasa.

Shugaban ya yi addu'ar Allah maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kurakuransa, ya ba shi masauki a Aljannar Firdausi, kuma ya ba iyalansa da duk waɗanda ke alhinin rashinsa haƙurin jure wannan rashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post