Limamai da Malamai 2,933 Ne Suka Hallara a Gidan Sanata Yari Domin Gudanar da Addu’o’in Neman Tazarcen Tinubu


Kimanin limamai da malamai 2,933 daga sassa daban-daban na Jihar Zamfara ne suka hallara a gidan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon Sanatan Zamfara ta Yamma, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, domin gudanar da addu’o’i, da neman nasarar Sanata Abdulaziz Abubakar Yari da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu 

Mahalarta taron, waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi da sassa daban-daban na jihar, sun gudanar da addu’o’i tare da roƙon Allah ya kawo zaman lafiya da tsaro da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Zamfara da Najeriya bakiɗaya tare da roƙon Allah ya ba wa Shugaban Kasa Bola Tinubu Nasara a shekarar 2027.

Addu’o’in sun kuma mayar da hankali kan neman Allah ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi wasu al’ummomin jihar, tare da roƙonsa ya kare al’umma daga dukkan nau’o’in fitina da masifa.

Taron ya samu halartar ɗimbin malamai da limamai, inda aka bayyana muhimmancin addu’a da haɗin kan al’umma wajen tunkarar ƙalubalen da jihar ke fuskanta.

An kuma yi kira ga al’ummar Zamfara da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai, tare da goyon bayan dukkan matakan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post