Gwamna Radda Ya Gabatar Ma Majalisar Dokokin Jihar Katsina Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 828.64 Na Ta Shekarar 2027

A ranar Talata 08/9/2026, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON ne ya gabatar da daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 na Naira biliyan ɗari takwas da ashirin da takwas da miliyan ɗari shidda (N828.64bn) ga Majalisar Dokokin Jihar.

kasafin kuɗin, wanda aka yi wa laƙabi da “Building Your Future IV”, ya sanya Katsina ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta kammala wannan mataki na tsarin shirya kasafin kuɗin shekara. 

Wannan ci gaba ya nuna yadda gwamnatin Gwamna Radda ta mayar da hankali kan bin ƙa’idojin kasafin kuɗi tare da tsara abubuwa tun da wuri da kuma tabbatar da ingantaccen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Daga cikin jimillar kuɗin kasafin, Naira biliyan 637.91, wanda ya kai kashi 76.98 cikin 100, an ware shi ne domin ayyukan raya ƙasa (Manyan Ayyuka), yayin da Naira biliyan 190.73, wato kashi 23.02 cikin 100, aka tanada domin ayyukan yau da kullum na gwamnati (Kuɗin Gudanarwa).

Kasafin kuɗin na 2027 ya ragu da kashi 7.71 cikin 100 idan aka kwatanta da kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka amince da shi. 

Gwamnatin ta yi wannan tsari ne bisa la’akari da hasashen samun kuɗaɗen shiga, buƙatun kashe kuɗi da kuma hanyoyin samun kuɗin gudanar da ayyukan gwamnati.

Gwamna Radda ya bayyana cewa an buƙaci Ma’aikatu, Hukumomi da Ƙungiyoyin Gwamnati (MDAs) su tsara buƙatun kashe kuɗaɗensu bisa tsarin ci gaba daidai da manufofin Building Your Future, da kuma kuɗaɗen da ake da su da kuma buƙatun da al’ummar jihar suka bayyana.

Gwamnan ya bayyana kasafin kuɗin 2027 a matsayin kasafin kuɗin da aka fi tuntuɓar jama’a a tarihin Jihar Katsina, inda ya ce an yi la’akari sosai da sakamakon Taron Tattaunawa da Jama’a kan Kasafin Kuɗi (Citizens’ Budget Exercise) da aka gudanar a dukkanin gundumomi 361 na jihar a ranar 18 ga Yuli, 2026.

A yayin wannan atisaye, jama’a sun bayyana tare da tantance da kuma fifita buƙatunsu mafiya muhimmanci. Inda aka ɗauki aikin da aka fi buƙata a kowace mazaɓa a matsayin wani muhimmin tsarin raya ƙasa daga tushe a kasafin kuɗin shekarar 2027.

Hakan na nufin cewa kowace mazaɓa daga cikin mazaɓu 361 za ta samu wani aiki na musamman wanda al’ummar yankin da kansu suka zaɓa. Haka kuma, bayanan da aka tattara za su taimaka wajen tsara ayyuka da tsare-tsare a fannonin noma, da kuma ƙanana da matsakaitan sana’o’i da kamfanoni (MSMEs) da ruwa da tsaftar muhalli (WASH), da  ƙarfafa mata, da kare muhalli da kuma sauyin yanayi da tsaro.

Dangane da rabon kasafin kuɗin bisa manyan ɓangarorin tattalin arziƙi da zamantakewa, Sashen Zamantakewa (Social Sector) an ware Naira biliyan 317.73, wanda ya kai kashi 38.34 cikin 100. Sashen Tattalin Arziƙi (Economic Sector) zai samu Naira biliyan 303.17, wato kashi 36.59 cikin 100, yayin da Sashen Gudanarwa (Administrative Sector) zai samu Naira biliyan 198.55. Sashen Shari’a da Adalci (Law and Justice) kuwa zai samu Naira biliyan 9.19.

Manyan fannoni biyar da aka bai wa fifiko za su samu jimillar Naira biliyan 325.45, wanda ya kai kashi 51.02 cikin 100 na jimillar kasafin kuɗin ayyukan raya ƙasa. 

Ayyukan sun haɗa da:

1. Ilimin Firamare da da Sakandire: Naira biliyan 83.82
2. Manyan Ayyuka: Naira biliyan 71.60
3. Noma da Kiwo: Naira biliyan 65.88
4. Kiwon Lafiya: Naira biliyan 53.64
5. Raya Karkara: Naira biliyan 50.51

Sauran Naira biliyan 312.47 za a karkatar da su ne zuwa wasu muhimman fannoni, ciki har da tsaro da tsarin gudanar da harkokin gwamnati ta hanyar fasahar zamani (e-Governance).

Da yake bayyana yadda aka aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2026, Gwamna Radda ya bayyana cewa jihar ta samu Naira biliyan 267.47 a matsayin kuɗaɗen shiga na yau da kullum, wanda yayi daidai da kashi 44.16 cikin 100 na abin da aka tsara za a samu. Haka kuma, an samu Naira biliyan 116.41 a matsayin kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa, wanda ya kai kashi 39.84 cikin 100 na abin da aka tsara.

Jimillar kuɗin da gwamnati ta kashe ya kai Naira biliyan 295.19, wato kashi 32.88 cikin 100 na jimillar kasafin kuɗin shekarar. Daga cikin wannan adadi, Naira biliyan 102.17 aka kashe wajen ayyukan yau da kullum, yayin da Naira biliyan 193.02 aka kashe wajen ayyukan raya ƙasa.

Gwamnatin jihar ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da Ayyukan Sabunta Birane na Katsina da Funtua, titin Musawa-Gingin-Tabanni, titin Kunduru-Kadanya, Daura Western Bypass, ayyukan samar da gidaje da kuma samar da manyan motoci 30 masu amfani da haɗaɗɗen makamashi.

Ilimi ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin ta bai wa fifiko. Gwamnatin ta ware Naira biliyan 13.03 domin gyara da sabunta makarantu ƙarƙashin shirin TESS, Naira biliyan 10.53 domin ayyukan inganta makarantun sakandare ƙarƙashin shirin AGILE, da kuma Naira biliyan 5.88 domin ayyukan makarantun firamare tare da haɗin gwiwar UBEC.

Haka kuma, za a kashe Naira biliyan 3.55 wajen makarantu na musamman guda uku, Naira biliyan 2.07 domin biyan kuɗaɗen jarrabawar SSCE, yayin da Naira biliyan 1.26 aka ware domin bayar da tallafin karatu ga ɗaliban da ke karatu a gida da ƙasashen waje.

A fannin kiwon lafiya, Jihar Katsina a halin yanzu tana da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, da na biyu da na uku guda 1,751, inda sama da kashi 85 cikin 100 daga cikinsu ke aiki yadda ya kamata.

Gwamnatin ta kashe Naira biliyan 4.71 wajen Shirin Ayyukan Gaggawa na Lafiya da Tsarin Motocin Asibiti (State Emergency Medical Service and Ambulance System Programme). Haka kuma, tun daga shekarar 2025, ta kashe sama da Naira biliyan 9.59 wajen samar da kayan aiki a Cibiyar Medical Imaging Centre da ke Babban Asibitin ƙwararru na General Amadi Rimi, wanda ake sauyawa zuwa cibiyar zamani ta kula da cutar daji da kuma binciken hoton cikin jiki.

A fannin noma, gwamnati ta ware Naira biliyan 21.43 domin sayen takin zamani, Naira miliyan 479.56 domin ban ruwa, Naira miliyan 441.26 domin samar da ingantattun iri, da kuma Naira miliyan 269.35 domin noman iri na musamman. Haka kuma, jihar ta kashe Naira biliyan 3.11 wajen gyara da samar da hanyoyin karkara domin sauƙaƙa safarar amfanin gona zuwa kasuwanni.

Dangane da tsaro, gwamnatin ta kashe Naira biliyan 1.34 wajen samar da kayan aikin tsaro, sannan Naira biliyan 6.16 wajen alawus-alawus da gudanar da ayyukan tsaro. Wannan ya sa jimillar kuɗaɗen da aka kashe kan harkokin tsaro a shekarar 2026 suka haura Naira biliyan 7.5.

Gwamna Radda ya amince da cewa har yanzu akwai ƙalubalen tsaro musamman a wasu garuruwa da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare. Sai dai ya bayyana cewa ci gaba da ɗaukar matakan tsaro sun taimaka wajen dawo da al’amuran yau da kullum a yankunan da abin ya shafa, tare da bai wa manoma damar komawa gonakinsu.

Gwamnan ya bayyana cewa har yanzu akwai ƙalubale a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, ruwa da tsaftar muhalli da kuma ababen more rayuwa.

Ya ce akwai buƙatar ƙara yawan ma’aikata da kayan koyarwa a makarantu, tare da magance matsalolin cutar zazzabin cizon sauro, rashin abinci mai gina jiki ga yara, lafiyar mata masu juna biyu da cututtukan da ruwa ke haddasawa. Haka kuma, ya ce har yanzu akwai matsin lamba wajen samar da isasshen ruwan sha ga jama’a.

Gwamna Radda ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na faɗaɗa cibiyoyin samar da tsaftataccen ruwan sha da hanyoyin rarraba shi, ciki har da Aikin Ruwan Zobe Phase 1B, tare da ci gaba da tabbatar da mayar da Katsina jiha ta farko a Najeriya da ta kawar da yin bahaya a fili.

Gwamnan ya kuma yaba wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, da sauran ’yan majalisar bisa kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwar da suke yi da bangaren zartarwa.

Ya jaddada muhimmancin sa ido da majalisa ke yi wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma amfani da kuɗaɗen al’umma cikin tsari da sanin ya kamata.

Gwamna Radda ya bayyana kwarin gwiwar cewa Majalisar Dokokin jihar za ta yi nazari tare da amincewa da Dokar Kasafin Kuɗin 2027 cikin lokaci, domin bai wa gwamnati damar fara aiwatar da ayyukan kasafin tun da wuri.

Gwamnan ya nuna godiyarsa ga bangaren shari’a, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin addini, jami’an tsaro, abokan hulɗar ci gaba da ma’aikatan gwamnati bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban Jihar Katsina.

Gwamna Radda ya bayyana cewa kasafin kuɗin “Building Your Future IV” ya kasance wani alƙawarin sanya jama’a a cikin tafiyar da gwamnati, tare da ci gaba da mai da hankali kan bunƙasa tattalin arziƙi mai ɗorewa, bunƙasa ɗan'adam, da raya ƙasa daga tushe da faɗaɗa ababen more rayuwa, da ƙarfafa tsarin zamantakewa da kuma inganta tsaro a faɗin Jihar Katsina.

Taron ya samu halartar jami’an gwamnati ciki hadda sakataren gwamnati, shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Katsina, kakakin majalisar dokoki, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, yan majalisu, Tsohon Gwamnan Borno, Konel Abdulmumin, Alh Tukur Jikamshi da sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post