Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda Ph.D, ya ƙaddamar da rabon Conditional Cash Transfer (CCT) ga mutane dubu biyar da saba'in da biyar (5,075), ya ƙaddanar da tallafin ne domin inganta makarantu 66, da kuma kayan karatu ga yara marasa galihu a faɗin jihar.
Gwamna Radda ya bayyana cewa ɗalibai 12,675 za su samu littattafan rubutu, fensir, takalman makaranta da jakunkuna, domin rage matsalolin da ke hana yara zuwa makaranta.
Ya ƙara da cewa, ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa. Ya ci gaba da cewa wannan tallafin yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatinmu na tabbatar da cewa babu wani yaro da rashin hali ko kayan makaranta za su hana shi zuwa makaranta ko karatu.
Shugaban School- Based Management Committee (SBMC) na ƙasa, Alhaji Abdullahi Umar Wazirin Gwandu, ya yabawa gwamnatin Katsina kan ƙoƙarin inganta ilimi, yana jaddada muhimmancinsa hannun al’umma wajen kula da makarantu.
Shi ma Wakilin UBEC na Arewa maso Yamma ya yaba da ci gaban da Katsina ta samu, musamman wajen ɗaukar malamai da bunƙasa kayayyakin more rayuwa na makarantu. Ya kuma buƙaci a ci gaba da ɗaukar malamai bisa buƙatun al’umma domin rage giɓin malamai tsakanin birane da karkara.
Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Hon. Yusuf Suleiman Jibia, da Babban Sakatare na SUBEB, Dr. Kabir Magaji Gafiya, sun gode wa Gwamna Radda kan goyon bayan da yake bai wa fannin ilimi, tare da tabbatar da cewa tallafin zai taimaka wajen ƙara yawan zuwa makaranta da inganta koyo.