Kamfanin Apple Ya Kaddamar Da Wayar iPhone Duo Mai Lankwasawa Kan Dala $1,999

 Kamfanin Apple ya ƙaddamar da iPhone Duo, wayarsa ta farko mai lanƙwasawa, wadda farashinta zai fara daga dala $1,999.

Kamfanin Apple

Wayar tana da siffa da girman da ya yi kama da fasfo idan an naɗe ta, amma idan aka buɗe ta tana zama da babban allo mai girman inci 7.6. Haka kuma tana da ƙaramin allo mai girman inci 5.4 a waje idan an rufe ta.

Apple ta ce iPhone Duo tana amfani da sabon A20 Pro chip, tana da tsarin hinge na musamman, kuma an tsara ta domin sauƙaƙa ayyuka kamar amfani da manhajoji fiye da ɗaya a lokaci guda. Wayar za ta fara karɓar pre-order ranar 16 ga Oktoba, sannan a fara sayar da ita ranar 23 ga Oktoba, 2026.

Wannan ƙaddamarwa tana nuna babbar shiga da Apple ta yi cikin kasuwar wayoyin hannu masu lanƙwasawa, inda za ta fafata da kamfanoni kamar Samsung waɗanda suka daɗe suna kera irin waɗannan wayoyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post