Najeriya ta yi Alla-wadai da harin da yan Houthi su ka kai wa Saudiyya

Najeriya ta yi Allah-wadai da harin da mayakan Houthi na Yemen suka kai wa Masarautar Saudiyya a ranar 7 ga Satumba, 2026.

Houthi

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce harin ya jikkata fararen hula da dama tare da lalata wasu muhimman ababen more rayuwar jama’a.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Oluwafemi Adeniyi, ya bayyana cewa Najeriya na kallon harin a matsayin babbar barazana ga tsaron da ikon mallakar Saudiyya, da kuma zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Najeriya ta yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su mutunta dokokin kasa da kasa, su nuna kamun kai, tare da guje wa matakan da za su kara dagula rikicin ko jefa rayukan fararen hula cikin hadari.

Gwamnatin Najeriya ta kuma bayyana goyon bayanta ga Saudiyya, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post