Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta kakaba wa kamfanin jirgin sama na RwandAir takunkumi saboda karya wasu ƙa’idojin kare haƙƙin fasinjoji.
Mai magana da yawun NCAA, Michael Achimugu, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a.
Hukumar ta ci tarar kamfanin Naira miliyan 15 saboda gazawarsa wajen warware ƙorafin wani fasinja kan kayansa cikin wa’adin da doka ta tanada.
NCAA ta ce matakin ya biyo bayan gazawar kamfanin wajen magance matsalar kayan fasinjan bisa tanade-tanaden dokokin kare haƙƙin masu amfani da harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya.
Bugu da ƙari, hukumar ta umarci RwandAir da ya sauya wa fasinjan kayansa da suka lalace, tare da biyan shi dala 170 a matsayin diyya ta farko da ake tanadar wa fasinja domin biyan buƙatun gaggawa.
NCAA ta ce wannan diyya ta yi daidai da tanade-tanaden Sashe na 19 na Dokokin NCAA na shekarar 2023, wanda ya tanadi diyya da sauran hanyoyin magance matsalolin da fasinjoji ke fuskanta sakamakon matsalolin kaya.
Hukumar ta bayyana cewa matakin ya nuna ƙudurin ta na tabbatar da bin dokokin kare haƙƙin fasinjoji da kuma tabbatar da cewa kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Najeriya suna magance ƙorafe-ƙorafen fasinjoji cikin wa’adin da doka ta tanada.
A lokuta daban-daban, NCAA ta kakaba wa kamfanonin jiragen sama na cikin gida da na ƙasashen waje takunkumi saboda karya dokoki daban-daban.
Hukumar ta ce: “NCAA ta kakaba wa RwandAir takunkumi saboda karya dokokin kare haƙƙin masu amfani. An ci tarar kamfanin Naira miliyan 15 saboda gazawarsa wajen warware matsalar kaya cikin wa’adin da aka tanada.
“Bugu da ƙari, an umarci RwandAir da ya sauya jakar fasinjan da ta lalace, tare da biyan dala 170 a matsayin diyya ta farko, kamar yadda Sashe na 19 na Dokokin NCAA na 2023 ya tanada.”
Kamar RwandAir, NCAA ta kuma kakaba wa wasu kamfanonin jiragen sama biyar takunkumi a watan Fabrairun 2025 saboda laifuka daban-daban, inda aka tanadi hukunci mabambanta a kansu.
Kamfanonin da abin ya shafa sun haɗa da Royal Air Maroc, Arik Air, Ethiopian Airlines, Aero Contractors da Air Peace.
Kimanin mako guda kafin wannan mataki, hukumar ta yi gargaɗin cewa kamfanonin jiragen sama da suka gaza aiwatar da mayar da kuɗin fasinjoji cikin wa’adin da Sashe na 19 na Dokokin NCAA na 2023 ya tanada za su fuskanci takunkumi.