Rundunar ’yansandan Jihar Kano, ta kama wani mutum mai suna Adamu Musa, ɗan shekara 35 a duniya, bisa zargin kiran kansa da babban jami’in ’yansanda, tare da yin amfani da sunan yana damfarar jama’a.
Rundunar ta ce wanda ake zargin yana iƙirarin cewa shi CSP ne, kuma yana karɓar kuɗi da sunan zai taimaka wa mutane samun aikin ɗansanda ko kuma sauyawa mutane wajen yin aiki.
An kama shi a ranar 1 ga watan Satumba 2026, bayan samun bayanan sirri, inda aka gudanar da bincike a gidansa tare da ƙwato kakin ’yansanda na boge da kuɗi Naira 300,000.
Rundunar ta ce za ta gurfanar da shi a gaban kotu bayan ta kammala bincike.
Tags
Labarai