An Gurfanar da Tsohon da Ya Kai Wa Alkali Sara da Adda a Kotu

An sake gurfanar da wani tsoho mai shekaru 87 a gaban ƙuliya. Dattijon mai suna Ɗahiru Garba, ya gurfana a gaban kotu ne a Adamawa bisa zargin kai wa wani alƙali hari da adda a cikin kotu.
‎A cewar jaridar Gaskiya News Hausa, lamarin ya faru ne ranar 31 ga Agusta, 2026, a Kotun yankin Mayo-Ine da ke ƙaramar hukumar Fufore, yayin da Alƙali Dauda Hamman ke jagorantar wata shari’a.
‎Rahotanni sun ce Ɗahiru, wanda ya fito daga ƙauyen Korawa, ya taso wa alƙalin ne haiƙan da adda tsirara ba zato ba tsammani, inda ya sassara masa addar sau da dama. Harin Da tsohon ya kai masa, ya yi sanadiyyar munanan raunuka, wanda har ya kai ga an yanke masa hannu.
Sai dai daga bisani, ‎an kama wanda ake zargi da laifin, an kuma gurfanar da shi a Babbar Kotun Majistare ta 1 da ke Yola ranar Litinin. A yayin zaman kotun, Ɗahiru ya ce sharrin Shaiɗan ne ya sa shi aikata wannan katafare  laifin, ya kuma bayyana damuwa da nuna nadamar abin da ya aikata.
‎ASP Zakka Musa, wanda ya gurfanar da shi, ya gabatar da Rahoton Farko na ’yansanda, inda wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya aikata laifin. Daga bisani, an tura batun zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike.
‎A cewar ’yansanda, Alƙali Dauda Hamman ya kai rahoton lamarin ne a Ofishin ’yansanda na Mayo-Ine ranar 31 ga Agusta. Daga ƙarshe, Kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Ɗahiru a gidan gyaran hali da ke Yola, tare da ɗage shari’ar zuwa 17 ga Satumba, 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post